Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan kasuwar Nijar sun soma yajin aiki
'Yan kasuwar Jamhuriyar Nijar sun fara yajin aiki na kwanaki biyu saboda kisan 'yan uwansu da suka zargin jami'an tsaro sun yi.
'Yan kasuwar sun ce za su nuna rashin jin dadinsu kan abin da ya faru a kasuwar Tagabati da ke Yamai inda wasu 'yan kasuwa uku da mace daya da ta je sayen kaya suka mutu sanadiyar tashin gobarar da suka yi zargin hayaki mai sa hawayen da aka harba ne ya haddasa.
Tuni gwamnati ta tabbatar da faruwar lamarin tana cewa mutum uku ne suka rasa rayukansu.
Kazalika gwamnatin kasar ta dora alhakin faruwar lamarin kan kungiyar farar hula da ta fito taron da gwamnati ta haramta musu, domin nuna kin amincewa da aniyar gwamnatin ta ci gaba da rufe wadanda suka yi badakalar kudin ma'aikatar tsaron kasar.