Hotunan Harry da Meghan a fitarsu ta aiki ta karshe a gidan sarauta

An wallafa

Yarima Harry da mai dakinsa Meghan sun yi fitarsu ta karshe a bainar jama'a a hidimar da sukan yi a matsayinsu na iyalan gidan sarauta a wajen wani taron addu'a da aka shirya a kan ranar Common Wealth a Mujami'ar Westminster Abbey ta birnin Landan.

Yarima Harry da Meghan sun isa wajen Sarauniya - wadda ita ce shugabar Common Wealth - Yariman Wales, da mai matsayin 'Duchess' ta Cornwall da 'Duke' da 'Duchess' ta Cambridge a Mujami'ar tsakiyar birnin London.

A ranar Asabar, ma'auratan sun halarci bikin kade-kade na Mountbatten a babban zauren taro na sarauta, wato Royal Albert Hall a birnin London, inda aka yi masu yabo da tafi.

Daga ranar 31 ga watan Maris ba za su daina gudanar da ayyuka a madadin Sarauniya ba. Cikin wata 12 za a sake duba shiriye-shiryen da aka yi.

A ranar Juma'ar makon da ya gabata, Meghan ta gana da dalibai a Dagenham da ke gabashin London, don halartar bikin Ranar Mata ta Duniya.

Ana iya ganinta a hoto na kasa, tana yin alamar daidaito tare da dalibai, domin alamta daidaito.

A wani jawabi da ta yi, ta shaida wa daliban makarantar cewa: "Duk yadda kake jin kai karami ne, ko kake jin kana kasa a matakin daukaka, ko da kuwa mene ne launin fatarka, ko mene ne jinsinka, kana da damar fadar albarkacin bakinka, kuma tabbas kana da 'yanci yin magana a kan abin da yake daidai''.

Wannan rana ce kuma , Yarima Harry ya gana da zakaran 'Formula 1' na duniya, Lewis Hamilton a lokacin ziyarar da ya kai a hukumance don bude gasar tseren motoci ta ''Silverstone Experience''.

Yammacin da ya gabata, masu rike da matsayin sarautar ta Sussex sun ja hankalin manema labarai yayin da suka halarci wani bikin bayar da kyautar yabo ta gidauniyar 'Endeavour' a gidan Mansion da ke birnin Landan, inda dandazon masu daukar hoto ke kokawar daukar hoto.

Hoto na sama daga Samir Hussein na Harry da Meghan ne suna yi wa juna kallon kuda, ya sami yabo a dandalin sada zumunta na intanet.

Ma'auratan sun halarci wajen bikin murnar nasarorin da tsofaffin sojojin da ba su lafiya da wadanda aka raunata.

Wannan shi ne karon farko da suka bayyana tare tun bayan da aka bayar da sanarwa a cikin watan Janairu cewa za su sauka daga matsayin manyan gidan sarauta

An bai wa ma'auratan kyautar yabo, tare da wani wanda ya sami nasara, wanda ya nuna murnarsa ta hanyar bayyana aniyarsa ta auren wata wadda yake kauna a wajen taron.

Ana iya ganin Harry da Meghan da wani dan wasan kwaikwayo Ross Kemp a hoto na kasa suna tafi game da wannan bayyana aniyar auren.

Harry, wanda ya kwashe shekara 10 yana aikin soja, zai ci gaba da rike mukamansa na Manjo, da Laftanar Kwamanda, da Sukwadaran Lida yayin da ya janye daga hidimar gidan sarauta, amma kuma za a dage matsayinsa na girmamawa na soja.

Ma'aurata sun yi niyyar rarraba lokacinsu tsakanin Birtaniya da Arewacin Amurka, kuma mia magana da yawunsu zai kasance a Birtaniya a kai a kai.

Za su kuma ci gaba da rike lakabobinsu na 'masu alfarma', amma ba za su rika amfani da su ba. Za su kuma daina yin amfani da alamar tasu ta "SussexRoyal" daga lokacin bazarar wannan shekara ta 2020.

A wajen wata sabgar kuma da suka aiwatar ba da daewa ba, yariman ya hadu da mawakin nan Jon Bon Jovi a ranar 28 ga watan Fabrairu a wani dakin daukar wake-wake da ke titin Abbey a birnin Landan, yayin da suka sake daukar hoton bayan wani faifan waka a wajen da jama'a ke keytara titi.

Jon Bon Jovi da yarima suna magana da makirufo lokacin da ake sake daukar wata waka.

Ana kuma sa ran Yarima Harry ya kasance a wajen tseren famfalakin birnin Landan da za a yi a cikin watan Afrilu a matsayinsa na uban kungiyar gasar, yayin da shi da Meghan za su halarci wata sabgar wasannin a Netherlands a cikin watan Mayu mai zuwa.