Hotunan halittun ruwa masu kayatarwa

An wallafa

Hotunan karkashin ruwa da suka yi fice wadanda aka dauka daga tekuna da koguna da kuma tafkuna.

Sama da hotuna 5,500 na karkashin ruwa ne suka shiga gasar manyan hotunan karkashin ruwan da suka yi ficen.

Masu daukar irin wannan hotuna daga kasashen duniya 70 ne suka aika hotunansu wannan gasa.

Kananan kofaye a cikin dusar kankara suna yawo a cikin ruwan Antarctica.

Asalin hoton, Greg Lecoeur

Bayanan hoto, Hoton Greg Lecoeur na karkashin ruwa da ya dauka na daga cikin hotunan da suka samu nasara a gasar hotunan karkashin ruwa da suka yi fice a 2020 inda ya dauki hoton wasu kifaye a cikin kankara a cikin ruwa suna yawo. An daki hoton ne a Antarctica.
Presentational white space
Hoton manyan kifaye suna zagaye bishiya a Bahamas.

Asalin hoton, Anita Kainrath

Bayanan hoto, Hoton Anita Kainrath, daga Austria ya yi nasara, inda ta dauki hoton wasu manyan kifaye suna zagaye wata bishiya a karkashin ruwa a Bahamas.
Presentational white space
Hoton wani kifi da ya bude baki

Asalin hoton, Pasquale Vassallo

Bayanan hoto, Pasquale Vassallo dan kasar Italiya hotonsa ya samu nasara a gasar hotunan inda ya dauki hoton wani kifi da daddare ya bude bakinsa a karkashin ruwa.
Presentational white space
Kifayen ruwa da ake cewa Rabbitfish

Asalin hoton, Nick More

Bayanan hoto, Hoton Nick More daga Devon ya samu nasara a cikin jerin hotonan da suka yi fice inda ya dauki hoton wasu kifaye masu ruwan dorawa-dorawa a jikinsu suna yawo a cikin wani ruwa shudi. Ya dauki hoton ne a Indonesia
Presentational white space
Kifi mai kama da doki

Asalin hoton, Nur Tucker

Bayanan hoto, Nur Tucker daga Wimbledon ya samu nasara shi ma a gasar Birtaniya ta hotunan karkashin ruwa da suka yi fice, inda ya dauki hoton wani kifi ya mike tsaye kamar doki a wani karkashin wani teku.
Presentational white space
Flavia Eberhard tana ninkaya

Asalin hoton, Zena Holloway

Bayanan hoto, Wannan hoton Zena Holloway 'yar kasar Brazil da ta dauka na Flavia Eberhard a Mexico, wata gwanar ninkaya kuma mai fafutukar kare muhalli na daga cikin hotonan baki da fari da suka samu nasara a gasar baje kolin hotunan.
Presentational white space
Tarkacen jirgin ruwan Georgios

Asalin hoton, Renee Capozzola

Bayanan hoto, Hoton Renee Capozzola ya samu nasarar shiga cikin jerin hotonan ruwa da suka yi fice a Birnitaya inda ya dauki wani tarkacen jirgin ruwa a Saudiyya.
Presentational white space
Wata dabba mai kama da doki da ke da kaho a goshinta

Asalin hoton, Keigo Kawamura

Bayanan hoto, Hoton Keigo Kawamura na wata dabba mai kama da doki kuma tana da kaho a goshinta shi ma ya samu nasara a gasar baje kolin hotona ta Birtaniya
Jewel anemones

Asalin hoton, Arthur Kingdon

Bayanan hoto, Shi ma hoton Arthur Kingdon na Jewel Anemones da aka dauka a tsibirin Scilly ya samu nasara.
Presentational white space
Hoton wani nau'in tsiro

Asalin hoton, Trevor Rees

Bayanan hoto, Hoton Trevor Rees na wani nau'in tsiro a Loch Dutch da ke yankin Shetland ya samu nasara a gasar baje kolin hotonan karkashin ruwa ta Birtaniya.
Presentational white space
Hoton wata dabba mai kama da kaguwa

Asalin hoton, Shane Keena

Bayanan hoto, Hoton Shane Keena da ta dauka na wata dabba mai kama da kaguwa wadda kuma ke amfani da gwangwanin da aka yar a gida a tsibirin Peleliu, shi ma ya samu nasara a gasar baje kolin hotonan karkashin ruwa ta Birtaniya.