Coronavirus: An rufe wasu garuruwa a Italiya

Yan suna gadi a asibitin Schiavonia, da ke kusa da Padova, inda a nan ake yin gwajin cutar coronavirus a lardin Veneto

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Yan suna gadi a asibitin Schiavonia, da ke kusa da Padova, inda a nan ake yin gwajin cutar coronavirus a lardin Veneto
An wallafa

An sanya dokar hana shiga da fita daga wasu garuruwa bayan rasuwar mutum biyu da suka kamu da cutar coronavirus a kasar Italiya.

Dokar ta rufe unguwannni fiye da ashirin a lardunan Laboardy da Veneto da ke arewacin kasar, inda aka umurci mazauna fiye da 50,000 da su lizimci gidajensu.

An rufe makarantu tare da soke dukkanin harkokin wasanni a yankunan da aka killace, ciki har da wasannin gasar kwallon kafa ta Serie A na ranar Lahadi.

Firai minista Giuseppe Conte ya sanar da sabuwar daokar yayin da 'yan kasar fiye da 100 suka kamu da cutar.

Mista Conte ya ce an haramta shiga ko fita daga yankunan da aka rufe, sai da izini na musamman daga hukuma.

Ya ce za a girke jami'an tsaro domin tabbatar da bin dokar, idan har hakan ta kama.

Dokar na daga cikin matakan da gwamnatin Italiya ta dauka na dakile yaduwar coronavirus a nahiyar Turai.

Firai minita Giuseppe Conte yana jarorantar taron gaggawa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Firai minitan Italiya Giuseppe Conte (a tsakiya) ya ce ba za bari mutane su shiga ko su fita daga yankunan da ke fuskantar barazanar coronavirus ba.

Hukumomin kasar na fargabar cutar ta yadu fiye da tsakanin dadaikun mutanen da suka kamu da ita a lardunan biyu kuma hakan zai kawo matsala wurin shawo kanta.

"Cutar na da matukar hadari kuma yaduwarta ta yi yawa,'' inji shugaban hukumar lafiya ta Lombardy Giulio Gallera.

Bakuwar cutar coronavirus da ta fara bulla a lardin Hubei na kasar Chana a shekarar 2019, ta yadu zuwa kasa 26, inda ta kashe mutum 11, wasu 1,400 kuma ke fama ita.