Najeriya na cikin kasashen da makomar yara ke cikin hatsari

Asalin hoton, Getty Images
Najeriya na cikin kasashen da makomar yara kanana ke cikin hatsari, kamar yadda sabon binciken da aka fitar kan makomar rayuwar yara kanana a duniya ya nuna.
Rahoton wanda Hukumar Lafiya ta Duniya da Asusun kula da kananan yara na Duniya, Unicef, da mujallar lafiya ta The Lancet suka fitar ya ce Najeriya ce kasa ta 174 cikin jerin kasashe 180 da aka yi nazari akansu game da bunkasar lafiya yara.
Hakan na nufin Najeriya na daya daga cikin kasashe goma na karshe a duniya da makomar yara ke fuskantar rashin tabbas ta fuskar bunkasar rayuwarsu da lafiyarsu.
Rahoton ya ce nazarinsa kan hatsarin da makomar yaran ke ciki ya dogara ne kan mizanin tsira da rai ga kananan yara da koshin lafiyarsu wadanda suka hada da lafiya da ilmi da abinci mai gina jiki da daidaito da tazarar da ke akwai ta fuskar kudin shiga.
Binciken ya ce sama da yara Biliyan biyu ke rayuwa a kasashen da ci gabansu ke fuskantar barazana daga rikici da bala'o'i da canjin yanayi ke haddasa wa.
Rahoton ya kwatanta kwazon kasashe 180 ne ta fuskar kosawar lafiyar kananan yara a kasashen, kuma Najeriya na kasan kasashe irinsu Afghanistan da Saliyo da kuma Sudan ta Kudu.
Rahoton mai taken "Ina makomar yara a duniya?" Ya gano cewa lafiya da makomar dukkan kananan yara da matasa a fadin duniya na cikin barazana a kurkusa daga gurbacewar rayuwar halittun muhalli da sauyin yanayi da kasuwancin ci da gumi da abincin kwalam da makulashe da lemukan zaki da barasa da taba sigari ga kananan yara.
A cewar rahoton babu wata kasa ko daya da za ta bugi kirjin cewa tana ba da isasshiyar kariya ga lafiyar yara da muhallinsu da makomarsu.
Alkalumma sun nuna cewa kananan yara a kasashen Norway da Koriya ta kudu da Netherlands ne ke da dama mafi kyawu ta tsira da rai da kuma koshin lafiyarsu, sabanin takwarorinsu a kasashen Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da Chadi da Somaliya da Nijar da Mali da ke cikin hali mafi muni.
Wakilin Asusun kula da kananan yara na Duniya a Nijeriya, Claes Johansson ya ce hakan na nuna irin kokarin da ke gaban Najeriya har yanzu don tabbatar da ganin yara a kasar na iya rayuwa cikin koshin lafiya a wani yanayi da za su iya habaka.
Ya ce sun sani cewa kashe kudi kan makomar yara da ba su ilmi da tabbatar da cewa suna da lafiya kuma suna samun abinci mai gina jikin da ya dace, aiki ne da zai kai ga samun ingantacciyar makoma ga kowa.
Rahoton ya gabatar da shawarwarin da suka kamata a bi cikin gaggawa don kare lafiyar yara da matasa a duniya. Ciki har da dakatar da fitar da gurbatacciyar iska cikin hanzari don tabbatar da ganin kanana yara suna da makoma.
Haka kuma rahoton ya bada shawarar sanya yara a tsakiyar kokarin da ake yi na cimma muradan ci gaba masu dorewa da bullo da sabbin manufofi da zuba jari a dukkan bangarori don cimma burin bunkasa lafiyar yara da kare 'yancinsu da shigar da yara cikin shawarwari kan manufofi da tsare-tsaren da suka shafi rayukansu.












