Harin Iran ya janyo karuwar masu matsalar kwakwalwa a sojin Amurka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumomi a Amurka sun ce adadin sojin kasar da suka samu rauni a kwakwalwarsu bayan harin da Iran ta kai sansanin sojinsu da ke Iraki a watan Janairu ya kai 109.

Wadannan alkaluma kari ne mai yawa a kan soji 64 da a baya hukumar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce sun samu rauni sanadiyar harin.

Tun da fari, Shugaba Donald Trump ya ce babu wani dan Amurka da ya ji rauni sakamakon harin.

Harin, wanda aka kai shi ranar takwas ga watan Janairu, ya faru ne sakamakon rikici da ya barke tsakanin kasashen biyu bayan Amurka ta hallaka kwamandan zaratan sojojin juyin-juya hali na Iran, Qasem Soleimani, a wani harin sama da sojojinta suka kai kan filin jirgin sama na Bagadaza, a Iraki.

Kusan kashi 70 na sojojin da suke sansanin lokacin harin sun koma bakin aiki, in ji wata sanarwa da Pentagon ta fitar.

Tun da fari dai Mr Trump ya ce ba su ji raunin ba ne a matakinsa na kin mayar da martani ga Iran.

Sai dai a watan da ya wuce, ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta ce ana samun karuwar masu matsalar kwakwalwa sakamakon raunin da suka ji a lokacin harin, hakan na nufin alamu sun fara bayyana na gagarumar matsala nan gaba.

A ranar Litinin 'yar majalisa ta jam'iyyar Republican Joni Ernst, ta ce suna bukatar karin bayani kan batun, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.

"Muna da tsarin da muke yi na bai wa sojojin nan kulawa, da yi musu magani kan cututtukan da ke damunsu.

''Ina kira ga ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta tabbatar da bai wa sojojinmu da aka kai wasu kasashe kariya da kulawar da ta dace, wadanda suke cikin barazanar samun raunuka sakamakon hare-hare da ake kai musu.''

A watan da ya gabata ne Shugaba Trump ya bayyana abin da yake ganin yana samun sojoji idan suka samu kansu cikin dimuwa da kaduwa sakamakon mummunan hari irin wanda Iran ta kai sansanin sojin Amurkar.

"Na ji an ce sukan yi fama da ciwon kai, da wasu abubuwan, zan iya cewa ba dai wata matsala ce mai ta da hankali ba,'' abin da ya fada kenan a lokacin da akai masa tambaya kan sojin da lamarin ya rutsa da su.

Da aka kara masa tambaya kan yiwuwar samun tabin hankali, Mista Trump cewa ya yi: ''Ba na jin ciwon da suka ji ya yi tsananin da har za a alakanta shi da tabin hankali.''

Me ake nufi da matsalar kwakwalwa sanadin harin bam?

Matsala ce gama gari musamman a yankunan da ake fama da yaki, kamar yadda rundunar sojin Amurka ta bayyana.

Ma'aikatar tsaron rundunar sojin Amurka ta rubuta wata makala, a ciki ta yi bayanin cewa karar fashewar bama-bamai ko makaman roka na daya daga cikin abin da kan gigita sojoji a fagen daga.

An kasa matsalolin kashi-kashi, akwai matsalar da ba ta yi tsanani ba, da kuma wadda ta wuce kima.

Karar fashewar wani abu, ko tashin wuta ko sauyawar sararin samaniya na haddasa dimuwa da tashin hankali.

Kara irin ta injin shara mai karar gaske kan sanya sojoji dimuwa da shiga tashin hankali a fagen daga, don hakan suke kauce wa abubuwa makamanta wannan saboda gudun samun matsalar kwakwalwa.

Gwamnatin Amurka ta ce bincike ya gano daga shekarar 2000, sama da sojoji 400,000 ne aka samu da tabin hankali.