Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kammala kada kuri'a a zaben 'yan majalisar Kamaru
An kammala kada kuri'a zaben zaben 'yan majalisar tarayya da na kananan hukumomi da aka yi a kasar Kamaru ranar Lahadi.
Kusan jam'iyyun siyasa 50 ne suka tsayar da 'yan takara a wadannan tagwayen zabukan da ake sa ran sabunta kujeru 180 na 'yan majalisar dokoki da kujeru sama da 10,000 na kansiloli a kananan hukumomi.
Bayan ya jefa kuri'a, Shugaban Kasa Paul Biya ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Na sauke nauyin da yake kaina kuma ina farin cikin yin hakan."
Shugaba Biya ya yi kira ga jama'ar kasar baki daya da su yi koyi da shi, sabanin kiraye-kirayen kaurace wa zabukan da wasu kananan jam'iyyun adawa suke yi.
Shi ma Mukaddashin Ministan kula da harkokin waje Felix Mbayu, wanda ya kada kuri'a a birnin Bamenda ya ce hanya guda wadda ita ce mafita domin magance rikicin da yankin renon Ingila yake fama da shi ita ce "jefa kuri'a".
Sai dai kuma, rashin tsaron da ake fama da shi a yankin rainon Ingila ya kai ga jama'a a birnin Kumba, na lardin kudu maso yamma, zaman gida saboda jin harbe-harben bindigogi da suke yi a sassan birnin.
Rahotonni na cewa masu fafutika da ke yunkurin kafa kasar Ambazoniya sun yi kaca-kaca da wasu motoci biyu na jami'an tsaro a garin Bafut na lardin arewa maso yamma.
Kazalika an ce sun je fadar basaraken garin domin hana jama'a fita zuwa kada kuri'a.
A yayin da aka bude rumfunan zabe a kan lokaci a wasu wurare, a wasu bangarorin kuma an samu jinkiri saboda rashin isowar cikakkun kayan zabe kamar tawadar dangwala yatsa.
Kusan kowanne sashe na kasan an sanya matakan tsaro, jami'an 'yan sanda da na jandarma suna tsaye cikin shirin ko-ta-kwana saboda barazanar da wasu jam'iyyun adawa irinsu MRC ta Maurice Kamto da CPP ta Edith Kah Walla suka yi.
Sun yi barazanar cewa ba za su shiga zaben ba, kuma za su nemi magoya bayansu kada su fita domin kada wata kuri'a.
Rahotanni na cewa, ta bangaren yankin rainon Ingila an ji harbe-harben makamai tun da asuba.
Sai dai ba a san ko artabu ne tsakanin jami'an tsaro da masu fafutuka da ke yunkurin kafa kasar Ambazoniya ba, wadanda su ma suka lashi takobin dakile gudanar da wani zabe a yankin da suka ce mallakinsu ne.
Har wa yau, an hade wasu mazabu da dama a wuri guda domin tabbatar da an samu shawo kan barazanar harin da 'yan aware suke yunkurin kaiwa.
Kakakin jam'iyyar adawa ta MRC Maurice Kamto wanda a yanzu yake kasar Canada, ya shugabanci wani taron manema labarai, inda ya yi Allah-wadai da abin da ya kira "kunnen uwar shegu da gwamnati take yi ga al'ummar yankin rainon Ingila".
Maurice Kamto ya yi zargin cewa a maimakon a fara neman warware matsalar da take addabarsu ta hanyar tattauanawa, kawai sai aka shirya wani zabe mai cike da kurakurai da dama.