Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane irin shiri kasashen Afirka suka yi wa Coronavirus?
- Marubuci, Daga Anne Soy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Nairobi
- An wallafa
Nahiyar Afirka na daya daga cikin nahiyoyi biyu da har yanzu ba a samu bulla cutar coronavirus ba, to amma kuma kwararru sun yi gargadin cewa ba lallai ba ne a ja tsawon lokaci ba a samu bullar tata ba idan aka yi la'akari da irin dangantakar da ke tsakanin China da kasashen Afirkan.
A kalla mutum 565 sun mutu yayin da aka tabbatar da kamuwar wasu dubu ashirin da takwas a fadin duniya, yawancinsu kuma a kasar China suke.
A makon da ya gabata, hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ayyana dokar ta baci a kan cutar, saboda fargabar bullar cutar a kasashen da ke fama da talauci.
Shugaban hukumar lafiyar Tedro Adhanom Ghebreyesus, ya ce " Babban dalilin da ya sa aka ayyana dokar ta baci a kan cutar shi ne, ba wai don abin da ke faruwa a China ba, a'a sai dai abin da ke faruwa a sauran kasashe."
Ya ce "Babban abin damuwar shi ne idan wannan cuta ta yadu a kasashen da ke da rauni a bangaren lafiya".
Tsarin kula da lafiya a yawancin kasashen Afirka na cikin wani yanayi tare da fama da wasu cutukan don haka ake ganin anya kuwa za su iya yaki da wata cutar idan ta bulla?
Michael Yao, shi ne shugaban agajin gaggawa na hukumar lafiyar a kasashen Afirka, ya ce wasu kasashen za su iya tunkarar duk wata cuta idan ta bulla.
Ko wadanne irin kayan aiki Afirka ke da shi a yanzu domin magance irin wannan cuta?
Tun kafin farkon makon da muka shiga, akwai manyan wuraren gwaje-gwaje guda biyu a Afirka, daya a Senegal da ya kuma a Afirka ta Kudu inda za a iya gwajin wannan cuta.
Daya daga cikin wuraren gwajin mai suna Institute Pasteur de Dakar, wanda ke kasar Senegal ya jima yana aiki a Afirka inda yake gwaje-gwajen cutuka da bincike a kansu.
A makon da muke ciki ne, kasashen Ghana da Madagascar da Najeriya da kuma Saliyo suka sanar da cewa su ma za su yi gwajin.
Hukumar Lafiya ta Duniyar ta aike da akwatunan kula da masu cutar coronavirus din ga wuraren gwaji ashirin da tara da ke nahiyar Afirka, domin tabbatar da cewa akwai abin da za a yi da zarar an samu wanda ya kamu da cutar.
Sannan kuma akwai fatan cewa, nan da zuwa karshen watan Fabrairun 2020, za a kai irin wannan akwatin ga kasashe 36 na Afirka, domin gwaji idan har an lura mutum na da alamomin cutar coronavirus din.
Dr Yao, ya ce "samun damar kasashen Afirka na gano cutar da wuri, ya danganta ne a kan kayan aikin da za a iya samu daga China da kuma kasashen Turai."
Kungiyar agaji ta Najeriya wato Nigerian Red Cross Society, ta ce ta sanya mutum miliyan daya da za su yi aikin sa kai wadanda za su kasance a cikin shirin ko-ta-kwana.
Sakatare janar na kungiyar, Abubakar Ahmed Kende, ya ce an dauki wannan mataki ne domin kare yiwuwar yaduwar wannan cuta a kasa.
A Tanzaniya, Ministar Lafiya ta kasar, Ummy Mwalimu, ta sanar da cewa, an samar da wasu cibiyoyi biyu da za a rinka kula da wadanda suka kamu da cutar idan har ta bullar a kasar a gabashi da kuma yammacin kasar.
Kazalika an samar da na'urar auna zafin jikin mutum fiye da 2,000 inda aka raba wa jami'an lafiyar da aka ba wa horo na musamman.
Kasashe da dama dasuka hada da Kenya da Habasha da Ivory Coast da kuma Botswana, sun yi maganin wadanda ake zargin sun kamu da cutar, inda suka kebe su a wani kebantaccen waje ana yi musu gwaje-gwaje daga bisani kuma aka tabbatar ba cutar coronavirus din ba ce.
Ma'aikatar lafiya ta Uganda ma, ta tabbatar da cewa, an kebe mutane fiye da 100 wadanda suka isa kasar ta filin jirgin saman Entebbe, inda aka kebe wasu a wasu asibitoci biyu da ke Entebbe da kuma Kamapala.
Yayin da sauran kuma aka ce musu su zauna a gida har sai an gama bincike da gwaje-gwaje.
Shin ko an samu wani darasi daga cutar Ebola?
Dr Yao na daga cikin wadanda suka taimaka wajen yaki da cutar Ebola a kasashen yammacin Afirka a shekarar 2014- 2016, dama inda aka yi yaki da cutar a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo a baya-bayan nan.
Ya ce yana da damuwa ganin cewa babu wasu kayan aikin da za a iya yakar mummunar cuta kamar coronavirus a Afirka.
Ya ce: "Muna shawartar kasashen Afirka da su rinka yin kokari wajen gano wadanda ke da alamun cutar coronavirus da wuri saboda gujewa yaduwarta".
Cutar Ebola ta sha bam-bam da cutar coronavirus, ita Ebola tana zama cuta ne idan har alamomin kamuwa da ita suka bayyana, ita kuwa coronavirus a kan kamu da ita ma ko da mai dauke da ita bai nuna wata alama ba".
Ko yaya za a yi da tafiye-tafiye tsakanin China da nahiyar Afirka?
Karuwar dangantakar kasuwanci a tsakanin China da kasashen Afirka na kara sanya damuwa kan yiwuwar yaduwar cutar zuwa Afirka.
China ita ce babbar abokiyar kasuwancin kasashen Afirka, kuma a yanzu haka akwai kamfanonin Chinan kusan 10,000 da suke aikinsu a nahiyar Afirka.
Kamfanin dillancin labaran Chinan ya ce akwai fiye da 'yan kasar miliyan daya da ke zaune a kasashen Afirka.
Kazalika akwai 'yan kasashen Afirka fiye da 80,000 da ke karatu a Chinar.
An rawaito cewa, wani dalibi dan kimanin shekara 21 da haihuwa dan kasar Kamaru ya kamu da cutar coronavirus bayan da ya je Wuhan inda yanzu haka ake masa magani.
Wata daliba 'yar kasar Zambiya Tisiliyani Salima, an kebe ta a wani waje fiye da mako biyu.
Ta ce a kullum idan ta tashi tana samun labarin cewa an kara samu wadanda suka mutu da wadanda suka kamu daga cutar coronavirus a Wuhan.
Duk da irin matakan da ake dauka a kan yaduwar cutar a birnin na Wuhan, har yanzu ana samun yaduwarta.
Daliban da suka fito daga kasashe kamar Najeriya da Zambiya da Tanzaniya da Kamaru da kuma Ivory Coast, sun fara cire rai a kan cewa gwamnatocin kasashensu za su aika a kwaso su.
Yawancin kamfanonin jiragen sama da ke sassan duniya sun dakatar da jiragensu daga zuwa China da ma tahowa daga China, abin da ya janyo ake matsawa kamfanonin jiragen saman Afirka da su ma su dauki irin wannan matakin.
Jiragen kasashen Masar da Kenya da Moroko da kuma Rwanda sun dakatar da jiragensu daga zuwa China, amma kuma kamfanin jirgin sama na Ethiopian Airlines, na ci gaba da zirga-zirgarsa.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da shawarar takaita tafiye-tafiye, inda ta bayyana muhimman kasashe 13 a Afirka, saboda alakar da ke tsakaninsu da China da rinka taka tsan-tsan da su.
Kasashen su ne:
- Aljeriya
- Angola
- Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo
- Habasha
- Ghana
- Ivory Coast
- Kenya
- Mauritius
- Najeriya
- Afirka Ta Kudu
- Tanzaniya
- Uganda
- Zambiya