An fara shirin kidayar jama'a a Saudiyya

saudi women

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An fara shirin aikin kidayar jama'a a Saudiyya mai taken ''Saudi Census 2020'' a ranar Litinin uku ga watan Fabrairu, inda za a kammala ranar shida ga watan Maris na 2020.

Kidayar, wadda za a shafe kwanaki 33 ana yi a fadin kasar, ta hada da kirga yawan mutane da gidaje da ma unguwanni.

Ana ganin wannan wani babban aiki ne kuma shi ne karo na biyar da za a yi kidaya a kasar.

Ana kallon wannan shiri a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan da suka shafi kidayar yawan jama'a da gidaje da gine-gine karo na biyar da aka taba yi a kasar, wacce aka yi wa take da Saudi Census 2020", kuma Hukumar Kididdiga ta kasar ce ta shirya.

An fara shirin kidayar ne a shekarar 2018, sannan za a fara yin ta ranar 17 ga watan Maris a kuma kammala ranar 6 ga watan Afrilu.

Manufar matakin kidayar gine-gine ita ce, tattara bayanai game da gine-gine da kuma muhallan da ake amfani da su tare da karkasa ma'aikatan da za su yi aikin da ma samar da bayanai game da gidaje da wadanda ke ciki.

An dai ba wa mutane fiye da 11,000 horo a kan yadda za su gudanar da aikin kidayar jama'ar da bayanansu gami da kidaya gine-gine da gidajen da ke fadin kasar.

Wannan kidayar da aka yi wa lakabi da ''Saudi Census 2020,'' ta sha bambam da sauran kidayar da aka yi a kasar.

Ko a cikin takardar da za a cike a yayin kidayar, akwai bukatar sanin muhimman bayanan mutum a ciki ba kamar sauran takardun da aka yi amfani da su wajen kidayar jama'a ba a baya a kasar.

Saudiyya dai ita ce kasa ta biyu a cikin kasashen Larabawa da take da girma.

Kidayar jama'a ta Saudi 2020

Asalin hoton, Global Media Insight