Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tarihin tsohon shugaban Kenya Daniel arap Moi
An haifi tsohon shugaban kasar kenya marigayi Daniel arap Moi ranar biyu ga watan Satumba na 1924.
Mr Moi ya hau karagar shugaban Kenya a 1978 bayan rasuwar shugaban kasar na farko Jomo Kenyatta.
Wannan ne karon farko da ya soma samun nasara a harkokin siyasa, inda ya yi wa fitattun 'yan siyasar kasar ba-zata wajen zama shugaban kasa.
Mr Moi mutum ne mai shiru-shiru
Irin wannan shiru-shiru nasa ne ya sa ya shafe shekara 24 yana mulki.
A farkon shekarun shugabancinsa, 'yan kasar ta Kenya sun hada hannu da shi domin gina kasar, inda ya yi amfani da wani salo mai taken 'Nyayo'', wanda a harshen Swahili ke nufin "bin sahu".
Moi yana da farn jini a tsakanin 'yan Kenya, musamman a wurin mutanen da ke kaunar ci gaba.
Amma bayan da aka yi yunkurin yi masa juyin mulki a 1982, Moi ya sauya zuwa mai mulkin kama-karya inda ya rika take 'yancin 'yan kasar da hana su fadin albarkacin baki.
An kama mutane da dama ba tare da wani dalili ba.
Daga nan kuma ya soma sanya kabilanaci da take hakkin dan adam da kuma kashe masu hamayya da mulkinsa.
A shekarar 1990 Shugaba Moi ya rikide ya zama cikakken mai kama-karya.
Sai dai kasashen duniya sun matsa masa lamba domin ya bar jam'iyya fiye da daya ta taka rawa a cikin harkokin siyasar kasar, sannan suka bukaci ya sanya wa'adi a tsarin mulki kasar.
Amma gwamnatinsa ta yi raddi ga masu zanga-zanga inda 'yan sanda rike da kulake suka rika dukan shugabannin jam'iyyun hamayya da magoya bayansu.
Bayan da ya raba kan 'yan hamayya ne, ya sake lashe zabe tsakanin 1992 zuwa 1997.
Gwamnatinsa ta yi fama da zarge-zargen cin hanci da rashawa - mafi shahara a cikinsu shi ne wanda ya biliyoyin dala ga wani kamfanin hakar gwal na boge, inda aka zarge da hannu kai tsaye a cikin batun.
Ya sha musanta zargin.
Bayan da wa'adin mulkinsa ya kare a 2002, Moi ya zabi dan lelensa Uhuru Kenyatta a matsayin mutumin da zai gaje shi.
Uhuru, wanda ake ganin a matsayin mutumin da ba shi da ra'ayi na kansa, ya sha kaye a hannun Mwai Kibaki.
Daga nan ne Moi ya yi ritaya daga harkokin siyasa kuma ya fuskanci ihu daga wurin dubban 'yan kasar ranar da ya mika mulki ga Kibaki.
Masu sharhi su ce ya ci gaba da yin tasiri a sha'anin siyasar Kenya ta bayan fage.
Kuma Moi ya yi sa'ar ganin Uhuru Kenyatta ya zama shugaban kasar a 2013.