Hukuncin shekara 99 ga mawakin da ya kashe mahaifiyarsa

An wallafa

An yanke wa wani matashin mawakin rap hukuncin shekara 99 a gidan yari bayan samunsa da laifin biyan kudi a kashe mahaifiyarsa.

Mawakin mai suna Qaw'mane Wilson mai lakabin Young QC, ya biya wani dan ina-da-kisa domin kashe Yolanda Holmes a shekarar 2012.

A ranar Juma'a ne aka yanke masa hukuncin a Chicago na kasar Amurka tare da sojan hayar tasa mai suna Eugene Spencer, wanda aka yanke masa hukuncin shekara 100.

Kotun ta saurari yadda Wilson ya yashe asusun bankin mahaifiyar tasa bayan rasuwarta.

"Kalmar 'matricide' na nufin mutum ya halaka mahaifiyarsa," Mai Shari'a Stanley Sacks na yankin Cook County ya fada a cikin kotun.

"Ta ba shi duk abin da yake bukata. Mota, aikin yi. Sai dai kawai a ce lalatacce ne. Ita ta yi wa Qaw'mane rai amma ya zabi ya kawo karshen tata rayuwar."

Bayan mutuwarta, Wilson ya kawata motarsa kirar Mustang, wadda mahaifiyar tasa ta saya masa.

An gabatar wa kotu shaidun yadda ya rika cirar kudi masu yawa sannan kuma ya rika watsa wa mutane a wani wurin wasansa na waka.

Wilson, dan shekara 23 a lokacin kisan, ya umarci Spencer ya shiga gidanta a Chicago, inda ya harbe ta yayin da take barci.

Lokacin da aka tambaye shi ko yana da abin fada kafin a bayyana hukuncin, Wilson ya ce: "Abin da zan ce kawai shi ne, babu wanda yake son mahaifiyata sama da ni. Ita kadai gare ni. Shikenan."