An kashe mutum 20 a turmutsutun ibada

An wallafa

Mutum 20 sun mutu a yau Lahadi sakamakon turmutsustu da aka samu a lokacin wani taron ibada a Tanzania.

Masu ibadar sun gamu da ajalinsu ne yayin rige-rigen taba mai mai albarka da limamin cocin ya zuba a kasa a lokacin ibadar da aka gudanar a wani filin wasa.

Shaidu sun bayyana wa 'yan jarida cewa lamarin ya auku ne yayin da masu bautar ke wucewa ta wata kofa da nufin tsallaka inda limamin coci ya zuba man.

A cewarsu, limamin cocin Fasto Boniface Mwamposa ya bukaci masu ibadar da su yi amfani da wata kofa inda ya sa mai mai albarka idan suka tashi fita daga filin taron.

Daruruwan mutane sun yi ta kokarin kaiwa domin taba man da nufin samun waraka daga cutuka.

Tuni 'yan sanda suka fara yi wa Fasto Boniface tambayoyi game da lamarin.

Shugaban kasar Tanzania Emmanuel Magafuli ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan sannan ya bukaci jami'an tsaro da su rika sanya ido wajen tabbatar da tsaron rayuka a duk sadda za a gudanar da manyan taruka a kasar.