'Yan Democrat na fuskantar koma baya kan tsige Trump

An wallafa

'Yan jam'iyyar Democrat a Amurka sun fuskanci babban koma baya a bukatarsu ta kiran shaidu a sauraren karar tsige Shugaba Trump.

Sun bukaci 'yan Republican hudu su mara masu baya, a kara bai wa wani shaida damar bayar da bayanai, amma daya daga cikin sanatocin da a baya yake inda-inda ya ce yanzu ba zai mara masu baya ba.

Lamar Alexander ya ce babu bukatar karin shaidu da za su tabbatar shugaban bai aikata laifin da za a iya tsige shi ba.

'Yan Democrat sun so musamman su ji daga bakin tsohon mai bai wa Shugaba Trump shawara kan harkokin tsaro, John Bolton.

Rahotanni sun bayyana cewa ya ce shugaban ya taba gaya masa baki da baki cewa ya dakatar da bai wa Ukraine agajin soji har sai ta amince ta yi bincike kan abokin hamyyarsa, Joe Biden.