An yi wa diyar Bill Gates baiko da Balaraben Masar

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Diyar fitaccen mai kudin duniyar nan Bill Gates, Jennifer ta sanar da cewar an yi baikonta da masoyinta dan kasar Masar, Nayel Nassar.

Jennifer da Nassar na soyayya tun a shekarar 2017 sannan suka yi baiko a wani wasan sululun cikin kankara da suka halarta.

Masoyan na wasanni irin na tsalle-tsalle da hawa doki suna kada su cikin duwatsu, sannan sun yi wasanni da dama tare a fadin duniya.

Jennifer, ta sanar a shafinta na Instagram cewa, "ta kosa ta ga lokacin da za su karasa rayuwarsu tare suna daukar darasi daga wurin juna, su rayu tare suna nishadi da soyayya".

Nayel a nasa shafin ma ya wallafa cewa, "na kagu mu ci gaba da rayuwa tare, sannan ba na tunanin rayuwa ba tare da ke ba".

Jennifer Gates mai shekara 23, daliba mai koyon aikin likitanci kuma mai son hawa doki a hirarta da kafar yada labarai na CNN, ta ce saurayinta na ba ta goyon baya ta kuma kara da cewa yadda suke son dawakai abu ne mai ban sha'awa.