Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sri Lanka: Kasar da ‘yan tagwaye ke son karya kwarin duniya
Wani yunkuri na ganin an gudanar da taron 'yan tagwaye mafi girma a Sri Lanka ya rushe bayan da yawan 'yan biyun da suka halarci bikin ya zarce tunani.
Wadanda suka shirya taron da aka yi wa lakabin ''Yan biyun Sri Lanka' sun yi kira ga taron 'yan tagwayen da su taru a filin wasa da ke Colombo, babban birnin kasar domin ganin sun karbe kambun taro mafi girma a Taiwan tun bayan wanda aka yi a shekarar 1999.
A wancan lokacin 'yan biyu 3,961 da 'yan uku 37 da kuma 'yan hudu guda hudu ne suka hallara a waje guda.
Amma a wannan karon, an samu tururuwar mutane da suka yi cincirindo a filin wasan ranar Litinin abin da ya haifar da dogayen layuka sannan kuma kokarin ganin an bi doka da oda ya ci tura.
'Yan biyu da dama ne suka halarci taron amma an samu dogayen layi wajen da ake tantance takardun shaidar haihuwa....
...inda akwai bukatar mahalarta taron su dauki hoto sannan su jira tsawon minti biyar.
Wadanda suka shirya taron na son su kafa tarihin taro mafi girma inda aka samu 'yan tagwaye 5,000 sun halarta.
Akwai 'yan tagwaye 14,000 da suke da rijista da kungiyar a Sri Lanka kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.
Wasu janar din soji Jayantha and Pooraka Seneviratne da su ma 'yan biyu ne...
...sun jagoranci gwamnan 'yan tagwaye daga rundunar sojin Sri Lanka.
Masu shirya taron sun ce yawan mutanen da aka samu a wajen taron ya sa ba su iya cika ka'idojin kafa tarihin ba a duniya.
... duk da saura makwanni biyu su gano ko za su iya kafa tarihi a kundin tarihin kamfanin Guinness.
Masu shirya taron sun sha alwashin shirya wani taron kuma akasarin mahalartan sun bayyana jin dadi da hakan.