Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Anthony Joshua ya yi gaisuwar ban girma ga Buhari
Wasu hotuna da suka watsu a kafafen sada zumunta sun nuna fitaccen dan wasan damben nan dan Birtaniya Anthony Joshua zube a kasa da ke nuna alamar gaisuwar ban girma irin ta kabilar Yarabawa ga Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a birnin London.
Joshua, wanda asalinsa dan Najeriya ne, ya fada wa jama'a cewa zai tsaya tsayin-daka wajen kare Najeriya a duk lokacin da aka bukaci hakan.
Mutane da dama sun bayyana mabambantan ra'ayoyi game da hotunan inda masu sukar Shugaba Buhari ke nuna takaici kan yadda dan damben ya ki bayyana irin dimbin kalubalen da matasan Najeriya ke fuskanta.
Sai dai tuni Joshua ya mayar da martani ta shafinsa na Instagram inda yace "wannan ba batu ne na siyasa ba. Batu ne na al'ada da kuma girmama na gaba da mu."
Wasu kuwa yaba wa Joshua suka yi kan yadda ya rungumi tsatsonsa Najeriya da kuma yadda ya nuna girmamawa ga Shugaba Buhari ta hanyar yin gaisuwar da aka san kabilar Yarabawa da yi.
Shugaba Buhari na birnin London domin halartar taron zuba jari na Birtaniya da Afirka na farko wanda aka fara ranar 20 ga watan Janairu.
Daya daga cikin masu taimaka wa Shugaba Buhari, Tolu Ogunlesi, ya wallafa wasu hotunan taron a shafinsa na Twitter inda ya ce: "AJ! Shi da shugaban kasa a yau."