Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wani bene ya rushe a Legas
Wani gini mai hawa biyu ya rushe a titin Ago Palace Way da ke Legas da misalin karfe shida na safiyar Juma'a.
Ma'aikatan agaji sun samu sun ceto mutum daya da ya makale a cikin baraguzan ginin, bayan dogon lokacin aikin ceto.
Rushewar ginin ta ritsa da shi ne a lokacin da yake barci, kamar yadda wasu mazauna unguwar suka shaida wa wakilin BBC.
Sauran mutanen da ke zaune a cikin ginin sun tsere, inda wasu suka samu kananan raunuka.
Babu wani bayani kan cewa mutumin na da rai ko ya mutu amma jami'an Hukumar LASEMA mai kula da muhalli a Legas na kokarin zaro shi.
Matsalar rushewar gine-gine a Najeriya
Yawan rushewar gine-gine da ake samu a Najeriya cikin shekaru ashirin da suka gabata abun damuwa ne matuka, saboda yadda ake samun asarar rayuka da dukiya sakamakon hakan.
Masana sun bayyana abubuwa da dama a matsayin wadanda ke jawo rushewar gine-ginen da suka hada da aikace-aikacen dan adam da kuma wata kaddara daga Ubangiji.
Hakan yana da matukar illa ga al'umma da kuma zuba jari a bangaren gine-gine.
Abubuwan da ke jawo rushewar gini
- Kayan gini marasa inganci
- Rashin aiki mai kyau
- Rashin saka tubali mai kyau
- Rashin amfani da kwararru a harkar gini
- Cin hanci da ya dabaibaye bangaren gine-gine
- Rashin bin ka'idojin da dokokin gine-gine
- Rashin kula
- Rashin bin shawarar kwararru
- Rashin tsara gini yadda ya kamata
- Dora kaya fiye da kima
- Mamakon ruwan sama
- Saba ka'idojin gini na hukuma.