Wani bene ya rushe a Legas

rushewar gini a Legas
An wallafa

Wani gini mai hawa biyu ya rushe a titin Ago Palace Way da ke Legas da misalin karfe shida na safiyar Juma'a.

Ma'aikatan agaji sun samu sun ceto mutum daya da ya makale a cikin baraguzan ginin, bayan dogon lokacin aikin ceto.

Rushewar ginin ta ritsa da shi ne a lokacin da yake barci, kamar yadda wasu mazauna unguwar suka shaida wa wakilin BBC.

Sauran mutanen da ke zaune a cikin ginin sun tsere, inda wasu suka samu kananan raunuka.

Babu wani bayani kan cewa mutumin na da rai ko ya mutu amma jami'an Hukumar LASEMA mai kula da muhalli a Legas na kokarin zaro shi.

Wannan layi ne

Matsalar rushewar gine-gine a Najeriya

Yawan rushewar gine-gine da ake samu a Najeriya cikin shekaru ashirin da suka gabata abun damuwa ne matuka, saboda yadda ake samun asarar rayuka da dukiya sakamakon hakan.

Masana sun bayyana abubuwa da dama a matsayin wadanda ke jawo rushewar gine-ginen da suka hada da aikace-aikacen dan adam da kuma wata kaddara daga Ubangiji.

Hakan yana da matukar illa ga al'umma da kuma zuba jari a bangaren gine-gine.

Abubuwan da ke jawo rushewar gini

  • Kayan gini marasa inganci
  • Rashin aiki mai kyau
  • Rashin saka tubali mai kyau
  • Rashin amfani da kwararru a harkar gini
  • Cin hanci da ya dabaibaye bangaren gine-gine
  • Rashin bin ka'idojin da dokokin gine-gine
  • Rashin kula
  • Rashin bin shawarar kwararru
  • Rashin tsara gini yadda ya kamata
  • Dora kaya fiye da kima
  • Mamakon ruwan sama
  • Saba ka'idojin gini na hukuma.