Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Libiya: An keta yarjejeniyar tsagaita wuta kasa da sa'a 24
Bangarorin da ke yakin basasa tsakaninsu a Libiya sun keta yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma.
Duka bangarorin biyu na zargin junansu da keta yarjejeniyar sa'o'i kadan bayan ta fara aiki.
Tun da farko dai bangarorin biyu sun amince da tsagaita wuta sakamakon matsin lambar da suka samu daga masu goya musu baya wato Turkiyya da Rasha.
Akwai bangaren Janar Khalifa Haftar wanda ke samun goyon baya daga kasar Rasha da kuma bangaren gwamnatin Tripoli da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta da kuma goya wa baya da ke mulki daga birnin Tripoli wanda shi ne babban birnin kasar.
A baya dai bangaren Janar Haftar sun yi watsi da kiran da aka yi na yin sulhu, a yanzu haka kuma sun bayyana cewa za su tsagaita wuta idan dayan bangaren ''ya bi yarjejeniyar tsagaita wutar yadda ya dace''.
A nata bangaren, gwamnatin Tripoli ta bayyana cewa za ta tsagaita wuta daga ranar Lahadi.
A makon da ya gabata ne dai Turkiyya ta tura sojojinta Libiya domin taimaka wa bangaren gwamnatin Tripoli mai samun goyon bayan MDD.
Rashin zaman lafiya ya lalata Libiya tun a 2011 bayan guguwar sauyin da ta yi waje da Tsohon Shugaban kasar Muammar Gaddafi.
Dakarun sojin da ke karkashin mulkin Janar Haftar na mulkar akasarin yankin gabashin Libiya inda suka nemi karbar babban birnin kasar a Afrilun 2019 amma hakan bai yiwu ba.
Amma a makon da ya gabata sun kwace gari na uku mafi girma a kasar wato Sirte.
A makon da ya gabata ne dai Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da kuma takwaransa na Rasha Vladimir Putin suka yi kira da a tsagaita wutar yakin basasar da ake gwabzawa a Libiya yayin wata tattaunawa da suka yi a birnin Santambul.