Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan tawayen Libya sun 'kwace' Sirte
Mayakan da ke biyayya ga jagoran 'yan tawayen Libya Janar Khalifa Haftar sun ce sun karbe ikon garin Sirte, a wani mataki da ake ganin gagarumar nasara ce kan gwamnatin Tripoli.
Tun 2016 da aka kori IS, Sirte ke karkashin ikon gwamnatin Tripoli da Majalisar Dinkin Duniya ke goyon baya.
'Yan tawayen da ke biyayya ga Janar Khalifa Haftar, sun dade suna kai farmaki da nufin kwace ikon Tripoli babban birnin Libya.
Babu wani martani daga gwamnatin Libya game da kwace garin na Sirte.
Wani mazaunin garin na Sirte ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa sun ga jerin gwamman motocin mayakan a lokacin da suke ta sinitiri bayan kwace garin.
A yanzu haka sune ke rike da yawancin garuruwan Libya, sai dai ban da wasu muhimmai da suka hadar da Tripoli inda nan gwamnatin da suke yaka ta yi sansani.
Tun kawar da Kanal Ghaddafi, Libya ke fama da yaki.
Me ke faruwa yanzu a Sirte ?
''Mun kwace baki dayan garin Sirte daga hannun 'yan ta'adda, in ji Ahmad al-Mesmari, wani mai magana da yawun mayakan Janar Khalifa Haftar yayin da yake bayani a kafar talabijin.
Wannan na zuwa ne bayan wasu wallafe-wallafe a shafin Facebook da kungiyar mayakan ta dingayi, inda take cewa ta kwace wasu muhimman wurare da suka kunshi har da da filin sauka da tashin jiragen sama.
Kuma yanzu haka tana ci gaba da samun nasara a kokarin tsarkake garin baki daya daga burbushin kungiyoyin masu dauke da makamai.
Garin na Sirte dai yana tsakiyar dakarun da ke adawa da gwamnati da kuma hukumomin da ke iko da gabashi da yammacin kasar.
Sirte kuma yana kusa da yankin Crescent mai arzikin mai.