Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Firai ministan Burtaniya ya gargadi Iran
Firai ministan Burtaniya, Boris Johnson ya ce Janar Qasem Soleimani da Amurka ta kashe makon da ya gabata "ya yi sanadiyyar kisan dakarun Burtaniya".
Mista Johnson wanda ya yi kira ga Amurka da Iran su mayar da wuka, ya shaida wa 'yan majalisar wakilai cewa Soleimani ne mai kitsa hare-haren da aka kai wa fararen hula da ba su san hawa ba ballanta sauka.
Ya kuma gargadi Iran da ka da ta maimaita 'gangancin' kai harin makamai masu linzami irin da wanda ta kai Iraqi.
Dakarun juyin-juya hali na Iran sun ce harin ramuwa ga kisan Soleimani.
Sai dai mista Johnson ya kara da cewa "Tabbas mun yi Alla-wadai da kai hari kan sansanin sojojin Amurka a Iraki".
To amma jagoran jam'iyyar hamayya ta Labour, Jeremy Corbyn ya dasa ayar tambaya dangane da makasudun kai harin jirgi maras matuki da Amurka ta bayar da umarnin kai wa boisa umarnin Shugaba Donald Trump wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Janar Qasem Soleimani.
Mista Corbyn ya kara da cewa ba alhakin Burtaniya ba ne nuna halasci ko akasin wannan hari "tun da ba abin da ya shafe mu ba ne."