Cardi B na son zama 'yar Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Mawakiyar nan Cardi B ta ce tana neman takardar shaidar zama 'yar Najeriya bayan da Amurka ta kashe Kwamandan Iran.
Mawakiyar 'yar Amurka mai salon wakar "rap" ta nemi shawarar masoyanta da su zabar mata suna irin na 'yan Najeriya.
Ta bayar da zabi guda biyu kan sunan da take so wato tsakanin Chioma B da kuma Cadijat.
An sake wallafa rubutun da tayi a tuwita fiye da sau 10,0000.
Jaridar Premium Times ta Najeriya ta ruwaito cewa an rada mata sunan Chioma B irin na 'yan Najeriya, a ziyararta ta farko da ta kai wa Najeriya a Disamban 2019, yayin da kuma jaridar ta ce masoyanta musulmai 'yan arewacin kasar, sun zabar mata sunan Cadijat.
A ranar uku ga watan Janairun shekarar nan ne Cardi B ta wallafa a shafinta na tuwita cewar, tana neman takardar shaidar zama 'yar kasar Najeriya bayan da Shugaba Trump na Amurka ya ba da umurnin kashe Kwamandan Iran Qasem Soleimani.
Shugaba Trump ya ce suna da tabbacin cewa, Soleimani na shirya kai hare-hare wa Amurka kuma sun kashe shi ne a harin jirgi da Amurkan ta kai wa Baghdad ranar Juma'a.
Mawakiyar tace wannan shi ne mafi munin mataki da Shugaba Trump ya taba dauka.
Kisan ya janyo tashin hankali a yankuna da dama, yayin da Iran ke barazanar 'ramuwar gayya'.











