Bam ya hallaka mutum 9 a kan iyakar Kamaru da Najeriya

An wallafa

Rundunar sojin Kamaru ta ce abun fashewar da ya hallaka mutum tara a Gamboru da ke makwabtaka da jihar Borno ba Boko Haram ba ne suka tayar da bam.

Sojojin sun ce bayan tsananta bincike sun gano cewa wasu kanana yara ne da ke wasa da gurneti suka haddasa al'amarin.

Mai magana da yawun rundunar sojin ta Kamaru Cyrille Serge Atonfack Guemo ya ce yara kanana guda biyu ne suna wasa sai suka tsinki gurnet inda suka kai kasuwa domin sayarwa, a inda gurnetin ya tashi.

Da farko dai kafafen yada labaran kasar sun ruwaito cewa kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai harin.

An zargi wasu 'yan mata masu dakon kaya tsakanin Kamaru da Najeriya da haddasa wannan aika-aikar.

Al'amarin dai ya faru ne a kan gadar El Beid, wadda ta raba iyakar kasashen Kamaru da Najeriya kusa da garin Fotokol wanda ya raunata mutum 29.

Cikin wadanda suka jikkata har da wadanda suka fada cikin ruwa.

Kungiyar Boko Haram na ci gaba da kai hara-hare a yankunan da ke cikin kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi duk da rundunar hadin gwiwar da kasashen suka kafa don yaki da kungiyar.

A ranar Asabar ne kuma kasar Chadi ta bayar da sanarwar janye sojojinta daga Najeriya, wadanda ke cikin rundunar ta hadin gwiwa.

Masana na ganin janyewar za ta kara bai wa Boko Haram damar ci gaba da kai hari kan al'umomin yankunan da dama.