Trump ya ce Iran za ta dandana kudarta

Asalin hoton, EPA
Magoya bayan Iran masu zanga-zanga a Iraki sun fara kafa tantuna da niyyar zaman dirshen a gaban ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Bagadaza.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa ba za su daina zanga-zangar ba, kuma ba za su bar gaban ofishin jakadancin ba har sai sojojin Amurka sun fice daga Iraki.
A ranar Talata ne wasu masu zanga-zanga suka cinna wuta a wasu sassan ofishin jakadancin Amurkar da ke Bagdaza biyo bayan wani hari ta sama da Amurka ta kai wa kungiyar mayakan sa-kai da Iran ke goya wa baya a Iraki.
Kimanin mayaka 25 ne suka mutu lokacin da Amurkan ta kai hare-haren a sansanin mayakan masu alaka da kungiyar Kataib Hezbollah a Iraki da Syria ranar Lahadi.
Harin saman da Amurkar ta kai na zuwa ne jim kadan bayan wasu hare-haren roka da aka kai wa sojojin Amurka wanda harin ya yi sanadiyar mutuwar wani farar hula Ba'Amurke.
Jagoran addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya caccaki Shugaba Trump bayan Trump din ya zargi Iran da kai hare-haren.
Jami'ai a Amurka sun bayyana cewa akwai dakarun kasar da dama da za a kara turawa zuwa yankin na Iraki sakamakon tayar da zaune tsaye da ake samu.
Ko a wasu jerin sakonnin Twitter da Trump din ya wallafa na murnar sabuwar shekara ya bayyana cewa Iran din za ta dandana kudarta sakamakon harin da ta kai.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Ya bayyana cewa sai ta ''gane kurenta'' dangane da hare-haren, inda ya ce ''wannan ba kashedi ba ne, barazana ce. Barka da Sabuwar Shekara."












