Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka ta kai hari kan mayakan Iran a Iraki da Syria
Amurka ta gudanar da wasu hare-haren sama kan mayakan kungiyar Kataib Hezbollah da kasar Iran ke mara wa baya a Iraki da Syria, a wani martani dangane da mutuwar wani dan Amurkar mai kwantaragi.
Majiyoyin jami'an tsaron Iraki sun ce akalla mayaka 25 na Kataib Hezbollah ne aka kashe sannan an jikkata fiye da mayakan guda 50 a wani harin sama da aka kai musu ranar Lahadi.
Amurka dai na daukar wannan kungiya da ta 'yan ta'adda'.
Wani harin roka a wani sansani da ke Kirkuk ya yi sanaidyyar kisan wani dan Amurka mai yin kwantaragi sannan ya jikkata karin wasu mutane ranar Juma'a.
Da yake magana a Washington ranar Lahadi, sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya gargadi Iran cewa Amurka za ta dauki fansa a duk lokacin da aka taba rai ko lafiyar Amurkawa.
Sakataren tsaron Amurka, Mark Esper ya shaida wa manema labarai cewa wani jirgin yaki kirar F-15 ya kai hare-hare har wuri biyar da ke da alaka da kungiyar Kataib Hezbollah.
Ma'aikatar tsaron Pentagon ta ce uku daga ciki sun kasance a yammacin Iraki sannan biyu kuma suna gabashin Syria.
Kataib Hezbollah dai wata kungiyar mayakan sa-kai ce ta mabiya mazhabar Shi'a da aka kafa a 2007 da ke samun goyon bayan kasar Iran.
Amurka na zargin cewa kungiyar na da alaka ta kut da dakarun Iran masu fafutukar kwato birnin Kudus.
Amurkar ta kara da cewa kungiyar ta sha karbar tallafi daga Iran wajen kai hare-hare ga abokan hamayyarta.
Kasar ta Amurka dai na zargin kasar Iran da samun karfin ikon juya akalar harkokin cikin gidan Iraki tun bayan da Amurkar ta tunbuke Saddam Hussain a 2003.