Mutum 15 sun mutu a hatsarin jirgin sama a Kazakhstan

An wallafa

Wani jirgin sama ya fado a Kazakhstan, inda akalla mutum 15 suka mutu sannan gommai suka jikkata.

Jirgin dai na Bel Air ya taso ne daga Almaty - birnin da ya fi kowanne girma a Kazakhstan, inda ya tunkari Nur-Sultan, babban birnin kasar to amma sai ya rikito jim kadan bayan tashinsa.

Yanzu haka fasinjoji 60 da suka tsallake rijiya da baya na karbar magani a asibiti..

Har kawo yanzu dai ba a iya tantance hakikanin abin da ya haddasa hatsarin jirgin ba.

Sai dai wani dan jaridar kamfanin dillancin labarai na Reuters wanda ya kasance kusa da inda hatsarin ya faru, ya ce akwai dusar kankara sosai a wurin.