Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin 2020

An wallafa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan kasafin kudin kasar na shekarar 2020, wanda ya kai naira tiriliyan 10,594,362,364,830.

Shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Talata, yayin da yake tsaka da bikin cika shekara 77 da haihuwa.

A watan Oktoban da ya wuce ne shugaban ya gabatar da daftarin kasafin kudin a gaban zauren Majalisar Dokokin kasar.

A farkon wannan watan ne kuma majalisar ta amince da shi, inda ta yi kari a kan abin da shugaban ya tura mata daga tiriliyan N10.33 zuwa N10.594.

Kamar yadda Majalisar ta amince, an shirya kasafin ne kan gangar man fetur miliyan 2.18 da za a hako a kullum, inda farashinta ya kama kan dala 57 a madadin dala 55 da shugaban ya aika da farko.

Har wa yau, an ayyana tashin farashin kayayyaki kan kashi 10.81% da kuma naira 305 a matsayin farashin dala kan kowace naira daya, kamar yadda aka aika tun farko.

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Sanata Ahmed Lawan da Honorabul Femi Gbajabiamila da Boss Mustapha duk sun shaida saka hannun a yau Talata.