Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasashe marasa arziki na fama da masu mummunar kina da kuma tamowa
Daya daga cikin uku na kasashe matalauta a duniya na fama da kiba mai yawa da kuma rashin cin abinci mai gina jiki a lokaci guda, wanda hakan ke jefa mutane da yawa cikin matsananciyar rama, kamar yadda rahoton The Lancet ya bayyana.
Rahoton ya ce matsalar na faruwa ne sakamakon cin abincin da aka sarrafa fiye da kima da kuma karancin motsa jiki.
Mawallafan rahoton na kira da aka wo sauyi ga tsarin sarrafa abinci na zamani, wanda suka ce yana haifar da matsalar.
Kasahsen da matsalar ta fi shafe su ne kasashen yankin Afrika da na nahiyar Asiya.
Rahoton ya yi kiyasin cewa kusan mutane biliyan biyu da miliyan dari uku ne a fadin duniya da suka hadar da yara da manya ke fama da mummunar kiba. Wasu yara miliyan 150 kuma na fama da matsalar rashin girma.
Kasashe da yawa masu karanci da matsakaicin samu na fama da duka matsalolin biyu a lokaci guda, wadda aka fi sani da matsalar tamowa da rashin cimaka.
Wannan na nufin kaso 20 cikin dari na mutanen na fama da mummunar kiba; kaso 30 cikin dari na yara 'yan kasa da shekara hudu kuma ba sa girma yadda ya kamata; yayin da ake ganin cewa kaso 20 cikin dari na mata ke fama da rashin kiba.
Al'ummomi da iyalai za su iya fama da wadannan matsaloli na tamowa, kazalika daidaikun mutane a lokuta daban-daban a rayuwarsu, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Rahoton ya ce, a shekarun 1990 kasashe 45 ne cikin 123 suka yi fama da wannan matsalar, yayin da kasashe 48 cikin 126 suka kamu a 2010.
By the 2010s, 14 countries with some of the lowest incomes in the world had developed this 'double problem' since the 1990s.
A shekarun 2010 kuma, kasashe 14 cikinsu har da masu kasashe karancin kudin shiga a duniya sun fara fama da matsalolin biyu ne tun daga 1990.
Tabarbarewar tsarin abinci.
Rahoton ya ce akwai bukatar gwamnatoci da Majalisar Dinkin Duniya da cibiyoyin ilimi su dauki mataki domin shawo kan matsalar, wadda ke nuni ga bukatar sauyin abinci.
Yadda mutane ke cin abinci makwalashe yana sauyawa.Yawaitar kantinan zamani, saukin samun abinci marar gina jiki, da kuma raguwar motsa jiki, na kara yawaitar mutane masu mummunar kiba.
Wadannan sauye-sauyen na haifar da matsala ga kasashen karanci da masu matsakaicin samun kudin shiga, har ma da masu wadata.
Duk da cewa yaran da basa girma yadda ya kamata na raguwa a wasu kasashen, ana alakanta rashin girma yadda ya kamata da cin abincin da aka sarrafa fiye da kima a yarinta.
"Muna fama da sabuwar matsalar abinci," inji babban daraktan sashen lura da abinci mai lafiya da gina jiki na Hukumar Lafiya ta Duniya Dakta Francesco Branca wanda ya jagoranci wallafa rahoton.
"Ba zamu iya rabe kasashe ba a matsayin masu karancin samu marasa abinci mai lafiya ko kuma masu samu sosai, amma kuma mu fi damuwa da batun kiba fiye da kima."
"Duka na'o'i rashin cin abinci mai lafiya na da abu daya - tsarin abincin da ya gaza wajen samar wa mutane lafiyayyen abinci, mai saukin kudi da saukin samu."
Dr Branca said changing this needed changes in food systems - from production and processing, through trade and distribution, pricing, marketing, and labelling, to consumption and waste.
Dakta Branca ya ce sauya wannan na bukatar sauya tsarin abinci- tun daga noma zuwa sarrafawa da kasuwanci, jigila da dillanci, sanya farashin har zuwa yadda ake sanaya masu alama da sauransu.
"Wajibi ne da sauya dukkan tsare-tsare masu alaka da tsarin abinci," a cewarsa.
Mene ne abinci mai cikakkiyar lafiya?
Rahoton ya ce shi ne abinci da akwai:
- ya kunshi 'ya'yan itatuwa da ganyayyaki da hatsi da dangin gyada mai yawa
- matsakaicin adadin abincin da ake samu daga dabbobi
- maman da aka sarrafa, amma mara yawa
- abinci da kayan sha da gishiri da sukari mara yawa
Irin wadannan abinci na rage hadarin samuwar rashin lafiyayyen abinci da rashin girma yadda ya kamata. Sannan yana ba wa jiki kariya daga kamuwa da cututtuka.