Sudan ta Kudu: Amurka za ta saka wa shugabanni takunkumi

An wallafa

Amurka za ta kakaba takunkumi a kan masu kawo tarnaki ga yunkurin samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu.

Ma'aikatar harkokin wajen Amaruka ta ce mutanen Sudan ta Kudu sun ci bakar wuya sakamakon jan kafar da shugabannin kasar ke yi wurin wanzar da zaman lafiya a kasar.

A don haka ta ce za ta haramta wa duk mai kawo cikas ga samun zaman lafiya a Sudan ta Kudu shiga kasarta.

Ma'aikatar ta ce ya kamata shugabannin Sudan ta Kudu su sasanta tare da sadaukar da wasu bukatunsu saboda al'ummar kasar.

A halin yanzu Amurka na duba yiwuwar sauya matsayinta game da Sudan ta Kudu bayan cikar wa'adin da aka bai wa Shugaba Salva Kiir da jagoran 'yan tawaye Riek Machar.

Wa'adin ya tanadi cewa a kafa gwamnatin hadin gwiwa a yarjejeniyar zaman lafiyar da a aka yi a shekarar da ta gabata.

Mutanen biyu sun ce za su kafa gwamnatin hadin gwiwar a watan Fabarairu.

"Duk mutanen da suka kawo tarnaki kai tsaye ko a kaikaice ga zaman lafiyar.... za a hana su biza," inji ma'aikatar harkokin wajen Amurka.

Laifukan da za su janyo takunkumin sun hada da:

  • Saba yarjejeniyar tsagaita wuta ko yi wa juna kallon hadarin kaji.
  • Keta takunkumin sayar da makamai na Majalisar Dinkin Duniya.
  • Yin wata almundahanar da za ta tayar da fitina.
  • Tauye hakkin fadin albarkacin baki ko mu'amala ko tarayya ko gudanar da taro ko wani nau'i na tauye hakki.
  • Saba yarjejeniyar da aka sanya wa hannu.