Yadda za a kona sinadarin Calorie ta hanyar motsa jiki

Mutane na raba pizza domin su ci

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Michelle Roberts
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health editor, BBC News online
  • An wallafa

Masu bincike a Birtaniya sun ce ya kamata a rika lika gargadin yawan motsa jikin da ake bukata mutum ya yi don kona sinadarin Calorie da ke cikin abinci a makunshin abincin.

Fahimtar cewa, sai an yi tafiya ta sa'a hudu ake kona sinadarin Calorie da ke cikin pizza, ko gudun minti 22 don kona sinadarin Calorie da ke cikin cakulan, za ta fadakar da mutane.

Bincike ya nuna cewa, yin haka zai matukar taimaka wa mutane su rika kona sinadarin Calorie.

Sinadarin Calorie dai shi ne sinadarin da ke sanya kiba a cikin abinci.

Masana sun ce manufar hakan shi ne a rika karfafa gwiwar mutane su rika cin abinci mai gina jiki tare da kokarin rage kiba.

Wasu masu bincike daga jami'ar Loughborough, sun ce irin wannan motsa jikin zai rika rage sinadarin Calorie kusan 200 a jikin mutum idan dai har yana cin abincin da ke sanya kiba.

Dangane da sinadarin Calorie

  • Ana auna yawan abincin da zai sa sanya kuzari a jikin kowanne mutum ta wajen auna sinadarin Calorie.
  • Maza na bukatar sinadarin Calorie 2,500 a rana, yayin da mata kuma ke bukatar 2000 kawai, wanda hakan zai sa su samu karfi da kuzari a jikinsu.
  • Yawan cin kayayyaki ko abincin da ke dauke da sinadarin Calorie mai yawa ba tare da motsa jiki ba, na janyo mummunar kiba.

Wannan ya nuna yadda yakamata mutane su rika kula wajen cin kayan abinci ko sha tare kuma da motsa jiki.

Fiye da kaso biyu cikin uku na mutanen birtaniya da suka haura shekara talatin, suna da kiba kuma kibar ta su ta wuce hankali.

Wannan layi ne

Farfesa Amanda Daley, ta ce 'Suna bukatar su ji ra'ayoyin mutane a kan abin da suke ci da kuma yadda suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum'.

Nau'ikan abinci wadanda aka lika takardar yadda yawan motsa jikin da mutum zai yi don kona sinadarin Calorie, na taimakawa matuka wajen zabar abincin da mutum zai ci da ma yawan mosta jikin da zai yi.

Farfesar ta bayar da misalin cewa, idan mutum ya sayi cakulan mai dauke da sinadarin Calorie da yawansa ya kai 500, to a ka'ida ya kamata ya yi gudun minti 50 don kona sinadarin Calorie da ba ya bukata a jikinsa.

Wannan layi ne

Wannan ba abu ne da ya shafi rashin cin abinci ba, abu ne da ya shafi abin da za ka ci da kuma yawan motsa jikin da kake bukata a jikinka.

Wannan ya sa, masana ke ganin akwai bukatar wayar da kan mutane a game da abin da za su ci ko su sha, don kona sinadarin Calorie da ba sa bukata a jikinsu.