Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Pelosi ta ce za a ci gaba da shirin tsige Trump
Shugabar majalisar wakilai Nancy Pelosi ta ce 'yan majalisar za su gabatar da takardar tsige Shugaba Donald Trump kan laifin amfani da karfin iko, ba bisa ka'ida ba.
Pelosi ta kara da cewa "Dimokradiyyar mu na cikin tsaka mai wuya, don haka ya zama dole mu dauki mataki.
Shugaba Trump ya ce 'yan jam'iyyar Democrat sun haukace, tare da bukatar su gaggauta tsige shi idan hakan suke bukata.
A nasu bangaren, 'yan jam'iyyar Democrat din sun ce shugaban ya ci amanar rantsuwar kama aiki, ta hanyar rike tallafin da Amurka ke bai wa kasar Ukraine da sauran laifukan da suka shafi kudi.
Jam'iyyar Democrat dai ita ce take da gagarumin rinjaye a majalisar wakilan Amurka, hakan ya sa wasu ke ganin akwai yiwuwar tsige shugaban a zauren.
Sai dai a halin da ake ciki babu alamun jam'iyyar Republican da ke iko da majalisar dattawa ta shirya kada kuri'ar tsige Mista Trump daga mukaminsa.
Me Pelosi ta ce?
'Yar majalisar da ta fito daga yankin California, kuma take rikon mukamin shugabar majalisar wakilai, ta shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa ''Komai a bayyane yake karara, shugaban kasa ya yi amfani da karfin kujerarsa ba bisa ka'ida ba don cimma bukatar kashin kansa da ta shafe siyasa."
"Kuma hakan ya sanya tsaron kasarmu cikin hadari, ta hanyar janye tallafin soji da shirya ganawa a ofishinsa a matsayin musaya kan binciken abokin hamayyarsa ta fuskar siyasa.''
Ta kara da cewa ''Abin takaici ne, ya sanya biyan bukatar ran sa fiye da muradun Amurkawa, a yau ina bai wa jagoran wannan bincike umarnin ya ci gaba da aikin tsige shugaban ta hanyar amfani da abin da doka ta tanada.''
'Yan jam'iyyar Democrat dai sun kagara su kada kuri'ar amincewa da tsige shugaban kafin karshen shekarar nan, yayin da ake sa ran majalisar dokoki ta kada kuri'a a farkon watan Janairun shekarar 2020.
A lokacin da Misis Pelosi ke barin taron manema labarai, ta bai wa wani dan jarida amsar tambayar da ya ma ta kan ko da gaske ne ta tsani Shugaba Trump?
''Ban tsani kowa ba,'' in ji ta.
''Har yanzu ina yi wa shugaban kasa addu'a a duk lokacin da na samu sarari. Don haka kada ka kara min magana irin wannan,'' in ji Pelosi.
Wane martani fadar White House ta mayar?
Mista Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter jim kadan bayan Misis Pelosi ta gama yi wa 'yan jarida jawabi: "Idan za ku tsige ni, to ku gaggauta yin hakan ko a yanzu, don mu samu adalci a majalisa, sannan lamura su koma daidai a kasarmu.''
Ita kuwa sakatariyar yada labaran fadar White House Stephaine Grisham, bayan kammala jawabin Pelosi cewa ta yi 'yan jam'iyyar Democrat sun ji kunya.
Ta kara da cewa ''Mun zuba ido, muna sauraren shari'ar adalci da majalisar dokoki za ta yi.''
''A lokacin ne za ku ga yadda mai kara yake bigewa da zama mai laifi,'' in ji Grisham.
A ranar Laraba ne kwararru kan shari'a su uku, suka shaida wa kwamitin shari'a na majalisa cewa matakin matsawa wata kasa lambar yin bincike kan wani mutum da Shugaba Trump ya yi ya saba wa doka kuma idan an same shi da laifi ya cancanci a tsige shi.
Dayan farfesan da shi ne cikon na hudu, ya ce abin da Mista Trump ya yi tabbas ya saba wa doka.
Amma bai kai a tsige shi daga mukami ba.
Wasu daga cikin zarge-zargen da za a duba kan Mista Trump su ne amfani da karfin kujerarsa ba bisa ka'ida ba da kokarin hana gudanar da bincike, da kuma yunkurin hana majalisa zaman sauraren ba'asi kan zargin.