Ana gagarumin yajin aiki kan tsarin fansho a Faransa
Ana gudanar da yajin aikin gama-gari a Faransa domin nuna adawa da sauye-sauye ga tsarin fansho da zai tilasta wa miliyoyin mutane yin ritaya ko kuma a datse musu albashi.
Kasar Faransar na iya fuskantar koma baya na tsawon kwanaki yayin da ma'aikatan bangaren sufuri da malamai suka shiga yajin aikin.
Yajin aikin dai ya shafi sufurin jiragen kasa da zirga-zirgar jiragen sama inda aka soke kashi 90 cikin 100 na jigilar jiragen kasa.
Ana sa ran makarantu da dama za su kasance a rufe.
Ana yajin aikin ne domin kalubalantar kudirin Shugaba Macron na kawo sabbin sauye-sauye a kasar
Rahotanni na cewa kashi daya bisa uku na al'ummar Faransa ne ke goyon bayan yi wa tsarin fansho garambawul, sai dai wasu kalilan ne ke tunanin gwamnati za ta yi nasara wajen aiwatar da sauye-sauyen.

Asalin hoton, Reuters







