Abdul Mahdi: Majalisar Iraki ta amince ya ajiye aikin Firai Minista

An wallafa

Majalisar Iraki ta amince da ajiye aikin da Firai Minista Abdul Mahdi ya yi, bayan an shafe watanni ana tashin hankali.

Ba a san wanda zai maye gurbin Abdul Mahdi ba. Kakakin majalisar ya ce za a bukaci Shugaba Barham Saleh ya bayyana wani sabon firai minista.

A wani labarin, Fafaroma ya soki muggan matakan da jami'an tsaro suka dauka na murkushe masu zanga-zanga.

An dai kashe kimanin mutum 400 tun bayan da tashin hankali ya barke a Bagadaza da wasu birane a farkon watan Oktoba.

Wasu dubban mutane kuma sun sami raunuka. 'Yan kasar ta Iraki na neman gwamnati ta samar da ayyukan yi, kana ta kawo karshen cin hanci da rashawa bayan inganta ayyukan da ke tabbatar da jin dadin al'umma.

Zanga-zangar ta ci gaba da gudana a Bagadaza da wasu birane zuwa ranar Lahadi.

Ofishin Adel Abdul Mahdi ne ya sanar da cewa zai mika takardar ajiye aikinsa ga majalisar kasar a ranar Juma'a, bayan da babban malamin Shi'a na kasar ya nemi a kafa sabuwar gwamnati.

Ayatollah Ali al-Sistani ya soki yadda jami'an tsaron kasar suka rika yin amfani da karfin da ya wuce kima wajen murkushe masu zanga-zangar, kuma ya bukaci 'yan majalisa da su janye goyon bayan da suke bai wa gwamnatin kasar.