Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Siyasar Netanyahu na fuskantar gagrumar barazana
Duk wani mai tunanin cewa yanke hukunci kan zargin rashawa da ake wa firaministan Isra'ila zai kawo karshen rikicin siyasa da kasar ta fada ciki a 'yan kwanakin nan, to da alama ya yi kuskure.
A ranar Alhamis firaminista Benjamin Netanyahu ya yi amon munanan kalamai a kan jami'an tsaron kasar bayan zarge-zargen rashawa da ake yi masa, ya kuma caccaki bangaren shari'a na kasar da kuma kafafen yada labaru wadanda yake ganin suna son ganin bayansa.
Ya yi zargin cewa 'yan sanda da masu gabatar da kara na kulla kutunguilar ganin sun tuntsurar da shi daga mulki.
Ya dai dauki wannan mataki ne yayin da bincike ke kara zafi, kuma ana sa ran zai ci gaba da irin wadannan kalamai yayin da aka shiga yanayi na tangal-tangal din siyasa a kasar.
Duk da cewa an raunana karfin Netanyahu, to amma har yanzu yana da sauran lokaci a kokarin sa na ceto harkokinsa na siyasa.
Inda rikicin yake
Babban alkalin kasar ne ya zayyana zarge-zargen da ake wa Netanyahu bayan kwashe shekara 3 ana binciken alakar firaministan da attajiran abokan huldarsa.
Ana zargin Netanyahu da karbar kyaututtuka masu tsada daga wasu mutane domin yi masu alfarma da kuma yin wasu abubuwa kawai na neman suna ne a kafafen yada labaru.
Mista Mandelblit ya jaddada cewa ba ana yin binciken ne domin cimma wata manufa ta siyasa ba.
Kalubalen siyasa
Mista Netanyahu da abokin hamayyar siyasarsa Benny Gantz duk sun gaza wajen kafa gwamnati bayan zagaye biyu na zabukan kasar da suka gaza kammaluwa.
Wanda hakan ke nuna yiwuwar cewa sai al'ummar kasar sun sake komawa runfunan zabe nan gaba.
Yanzu haka dai al'amura sun dogara ne a kan jagororin jam'iyyar Likud ta Mista Netanyahu. A baya dai suna nuna goyon bayansu ne gare shi, to amma akwai alamun cewa nan gaba kadan zai iya fuskantar turjiya daga cikin gida.
Ministan ilimi na kasar Gideon Saar ya bukaci da a kira zabe na shugabannin jam'iyyar domin sauya Netanyahu.