Benjamin Netanyahu na daf da rasa mukaminsa na Firai minista

An wallafa

Firai ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya ce a shirye ya ke ya shiga shirin kafa gwamnatin hadin gwuiwa tar da abokin adawarsa Benny Gantz.

Wannan matakin na Mista Netanyahu ya kasance gagarumin sauyi ne dga wanda ya so ya dauka, wanda kuma ya biyo bayan rashin nasarar da ya samu a zaben da aka yi ranar Talata.

Mista Gantz ya ki amincewa da tayin Mista Netanyahu

Benyamin Netanyahu da Benny Gantz sun gana da juna a wajen wani taro tunawa da marigayi tsohon Firai minista Shimon Peres.

Amma ba a jima da kammala taron ba sai suka fito da makaman siyasa - musamman ma wanda ya shafi zaben wanda zai jagoranci kasar - zaben da kuma ya gaza fitar da wanda ya lashe kuri'u kai tsaye.

Da alama Mista Netanyahu ya fara shiga cikin damuwa - damuwar rasa mukaminsa na Firai minista.

Abin da ya nuna haka shi ne yadda ya nemi abokin hamayyarsa a siyasance da ya amince su kafa gwamnatin hadin gwuiwa.

A wani sakon bidiyo da ya fitar, Mista Netanyahun ya tabbatar da abin da kowa ya sani a kasar - watau ba shi da isassun kuri'un da za su ba shi zarafin kafa gwamnati ba tare da hada kai da wasu jam'iyyun siyasa ba.

Amma Mista abokin hamayyar na sa, kuma shugaban jam'iyyar Blue and White mai sassaucin ra'ayi, Mista Benny Gantz ya ki amincewa da tayin na Mista Netanyahu.

A wata ganawa da yayi da manema labarai, Mista Gantz ya ce jam'iyyarsa ba za ta shiga hadaka da mutumin da ke fuskantar shari'ar cin hanci da rashawa ba.