Za a saka wa tituna 10 sunan Shugaba Emmerson Mnangagwa

Emmerson Mnangagwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, President Emmerson Mnangagwa rose to power in 2017
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Mutane a Zimbabwe na bayyana rashin jin dadinsu bayn da ta bayyana cewa gwamnatin kasar ta amince ta sauya sunayen wasu manyan tituna da gine-ginen kasar da sunan wadanda ta kira "gwarzayen kasa" - ciki har da layuka goma da za a sauya wa suna zuwa na Shugaba Emmerson Mnangagwa.

Yaancin wadanda za a karraman sun taka muhimmiyar rawa a yakin sunkuru da aka yi da gwamnatin tsiraru fararen fata da ta mulki kasar.

Daga bayan wadannan mutanen sun zama shaharrun 'yan kasa saboda rawar da suka taka na kwato wa kasar 'yancin kai.

Wasu daga cikin shugabannin da za a karrama sun hada da Shugaba Patrice Lumumba na Congo, da Jomo Kenyatta da Abdel Gamal Nasser, da kuma tsohon shugaban Cuba Fidel Castro da Leonid Brezhnev shugaban tsohuwar tarayyar Soviet da kuma marigayi Shugaba Mao Zedong na China.

Amma 'yan Zimbabwe da dama sun bayyana damuwarsu da lokacin da majalisar ministocin kasar ta bata tana tattauna sauya sunayen manyan hanyoyin kasar da gine-gine, bayan kasar na fuskantar matsalolin tattalin arziki.

Wani mai amfani da Twitter ya yi shagube cewa watakila yanzu farashin kaya zai fadi, kuma za a sami daidaito na sauyin kudaden Zimbabwe da na kasashen waje:

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Presentational white space

Wani kuma ya bayyana damuwarsa kan kudin da za a kashe domin sake wallafa sabbin sunayen:

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Presentational white space

Shi kuwa wannan sukar gwamnati ya yi domin abin da ya kira "kwarewa da amfani da lokaci da ta yi":

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Presentational white space

A halin yanzu Zimbabwe na fuskantar karancin kudade, dalilin da ya sa ta sake dawo da takardun kudin kasar na Zimbabwe Dollar, bayan da aka shafe shekara 10 ana amfani da kudaden Amurka da na Afirka ta Kudu a cikin kasar.

Me yasa Zimbabwe ke son sauye sunayen wasu tituna?

Kafin ta samu 'yancin kai, ana kiran Zimbabwe da sunana Rhodesia ne, kuma asalin sunan na wani dan mulkin mallaka dan Birtaniya ne Cecil Rhodes.

An sauaya sunan kasar bayan ta sami 'yancin kai a 1980, amma a birnin Harare (wanda a da ake kiransa Salisbury) har yau akwai wani titi mai suna Cecil John Rhodes Drive, wanda za a sauya sunansa zuwa Willie Musarurwa Drive, sunan wani fitaccen dan jaridar kasar.

Presentational grey line

Ga sunayen hanyoyi biyar da ke nuna irin sauyin da aka samu a kasar:

  • Speke Avenue, wanda aka saka domin karrma wani dan Birtaniya zai koma Agostinho Neto Avenue, sunan shugaban Angola na farko
  • Livingstone Avenue, wanda shi ma sunan wani baturen Birtaniya ne zai koma Oliver Tambo Avenue, sunan wani dan Afirka ta Kudu da ya yaki tsarin nuna bambancin lauyin fata
  • Fife Avenue, wanda suna wani yankin kasar Scotland ne zai koma Leonid Brezhnev Avenue, suna tsohon shugaban tsohuwar Tarayyar Soviet
  • Allan Wilson Road, sunan wani sojan Bitaniya ne, za a sauya masa suna zuwa Mgagao Camp Road, wanda suna wani sansanin mayakan da suka yaki gwamnatin tsiraru fararen fata ne