Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jam'iyyun Habasha za su yi maja
'Yan siyasa a jam'iyya mai mulkin kasar Habasha ta People's Revolutionary Democratic Front sun amince da wani shiri na kafa wata sabuwar jam'iyyar siyasa
Firai minista Abiy Ahmed ya fito yana mara wa wannan matakin na 'yan siyasar baya.
Mista Abiy ya ce jam'iyyar da aka sanya wa suna Ethiopian Prosperity Party, za ta taimaka wajen hada kan kabilun kasar wuri guda, kuma za ta hada kan 'yan kasar.
Yana son sabuwar jam'iyyar ta zama wata hanya da za ta jagoranci siyasar kasar, a madadin tsarin da aka shafe shekaru 30 ana bi na jam'iyyu masu alaka da manyan kabilun kasar.
Amma wani dan siyasa daga jam'iyyar Tigray People's Liberation Front, jam'iyyar da ta mamaye siyasar kasar kafin zuwan Mista Abiy, ya ce ba zai shiga sabuwar jam'iyyar ba.
Ya ce dalilinsa shi ne, shiga sabuwar jam'iyyar na iya dakushe karfin fada a-ji na bangaren siyasar da yake wakilta.
Firai minista Abiy ya aika da wani sako na Twitter, wanda a ciki yake cewa majar "wani muhimmin mataki ne a kokarinmu na hada karfinmu wuri guda, domin cimma makomar da muke bukatar ganin kasarmu ta cimma."