Benjamin Netanyahu: Ana tuhumar Firai minista da cin hanci da rashawa

Benjamin Netanyahu speaks at the Israeli parliament in Jerusalem on 20 November 2019

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Netanyahu ya ce bai aikata wani laifi ba, kuma ya ce tuhumar "hari ne na siyasa."
An wallafa

Babban mai shigar da kara ana Isra'ila na tuhumar Firai minista Benjamin Netanyahu da aikata laifukan cin hanci da rashawa, da wawura dukiyar kasa da kuma zamba cikin aminci.

Duka wadannan tuhume-tuhumen na cikin wasu shari'u uku ne masu alak da juna.

Ana tuhumar Mista netanyahu da karbar kyaututtuka daga wasu attajiran 'yan kasuwa, kuma a dalilin haka ya rika yin watanda da dukiyar kasar domin kafofin yada labarai su rika yaba masa.

Amma Firai ministan ya bayyana matakin a matsayin "yunkurin juyin mulki", kuma ya soki daukacin binciken da aka yi kan batun.

Ya kuma dage cewa ba zai ajiye mukaminsa ba tun da doka ba ta bukaci ya yi hakan ba.

A wani jawabi da yayi a talabijin, Mista Netanyahu ya ce hukumomin shari'a na kasar "ba sa son sanin gaskiya, sai dai suna son ganin baya na ne", kuma ya nemi 'yan kasar da su "binciki masu binike".

Tun da farko babban jami'i mai shigar da kara Avichai Mandelblit ya sanar da cewa ya dauki matakin ne bayan ya "dauki kokaci yaa nazarinsa", amma ya ce matakin ya tabbatar da cewa babu wanda ya fi karfi doka a Isra'ila.

File photo showing Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu and Attorney General Avichai Mandelblit at a cabinet meeting (19 May 2013)

Asalin hoton, Empics

Bayanan hoto, Benjamin Netanyahu da babban mai shigar da kara Avichai Mandelblit

Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Isra'ila ke fuskantar wata kiki-kaka ta siyasa bayan kammala zaben gama gari da aka yi a Afrilu da Satumba, zabukan da suka kasa samar da wanda yayi nasara.

A ranar Laraba abokin hamayyar Mista Netanyahu na siyasa, benny Gantz ya sanar da gazawarsa ta kafa hadakar jam'iyyun da za su ba shi damar kafa gwamnati.

Protesters against Mr Netanyahu outside the prime minister's residence in Israel

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga sun fita tituna suna sukar Mista netanyahu

Shugaban kasar Reuven Rivlin ya bukaci 'yan majaisar kasar da su amince da wani mutumin da zai jagoranci kasar domin kaucewa sake yin wani zabe na uku cikin shekara guda.

Supporters of Mr Netanyahu stand outside the prime minister's residence with signs

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A nan magoya bayan Mista netanyahu ne suka taru a kofar fadar Firai ministan kasar inda ske cewa bai aikata laifi ba