Birtaniya ta mayar da 'yan asalin Syria gida

An wallafa

Gwamnatin Birtaniya na shirin mayar da 'yan Birtaniya wadanda suka fito daga 'yankin Syria a tsohon yankin da IS ta mamaye, BBC ta samu labari.

Bisa wasu dalilai , BBC ba za ta iya bayyana cikakkun bayanai ba. Mutanen da suka fito daga yankin za a mayar da su kasarsu.

IS ta yi iko da yankin mai fadin kasa mil 34,000 wanda ya kama daga yammacin Syria zuwa gabashin Iraki.

Yadda za a yi da mayakan IS da wasu mayaka sauran kasashen waje wadanda rikicin ya rutsa da su na daga cikin manyan lamurra tun bayan da aka ci galabar IS a watan Maris na 2019.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya kamata kasashe su dauki alhakin kula da mutanensu idan ba hukunta su za a yi a Syria ba.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta bayyana shirin mayar da mutanen da wani "shiri maras tsari'.

Ta ce sama da mutum 1,200 daga kasashe da dama aka mayar zuwa Syria da Iraki da Kazakhstan da Uzbekistan da Tajikistan da Russia da Kosovo da kuma Turkiyya.