Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ganduje ya yi watsi da hukuncin kotu kan masarautu
Gwamnatin jihar Kano ta ce tana nazarin hukuncin babbar kotun da ta soke sabbin masarautu hudu da gwamnatin ta kirkira, domin daukar matakin da ya kamata.
Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar ta Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar, ta ce ta yi takaicin cewa duk da ikon da tsarin mulki ya bai wa majalisar jihar kan irin wannan batu na ci gaba, amma kotun ta yi watsi da komai. Sanarwar ta kara da cewa gwamnati ba za ta zura ido ba ta kuma sarayar da damar da take da ita wajen inganta rayuwar al'ummar jahar.
Malam Garba ya ce "duk da cewa kotun ta yanke wannan hukunci, to gwamnati za ta ci gaba da martaba sarakunan yankan sannan ta ci gaba da yin mu'amala da su."
Kotun dai ta rushe dokar da ta bai wa majalisar jihar Kano damar kirkiro sabbin masarautu ne a ranar Alhamis.
Babbar kotun jihar ta ce ta yanke wannan hukunci ne saboda an shigar da kudurin bukatar kirkirar masarautun ba bisa ka'ida ba.
Ga dukkan alamu dai wannan hukunci na babbar kotun na nufin yanzu sarki daya ne a Kano ba biyar ba kamar yadda aka kirkira a 'yan watannin da suka gabata.
Barista Ibrahim Mukhtar shi ne lauyan bangaren gwamnatin jihar, kuma ya shaida wa BBC cewa kotu ta yanke hukuncin ne ba tare da tsayawa ta yi bincike yadda ya kamata ba.
A watan Mayun 2019 ne gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da takardar kama aiki ga sabbin sarakunan jihar Kano da majalisar jihar ta gabatar da kudurin doka don kirkirarsu.
Sarakunan dai sun hada da Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Bichi da Ibrahim Abubakar a matsayin Sarkin Karaye sai Tafida Abubakar Ila Sarkin Rano da kuma Ibrahim Abdulkadir a matsayin Sarkin Gaya.
Wani lauya mai suna Ibrahim Salisu ne ya fara gabatar da bukatar kirkirar sabbin masarautun a Kano da sunan kamfaninsa. Kwanaki kadan da yin hakan ne kuma majalisar ta yi wani zama don tabbatar da dokar.
Amma a ranar Alhamis da take yanke hukuncin, kotun ta ce ba a san inda kamfanin nasa yake ba, kuma ya kasa bai wa kotun gamsasshiyar hujja game da koken nasa.
Ta kuma ce Ibrahim ba shi da hurumin da zai shigar da batun majalisa har a yanke hukunci cikin kwana uku.
Kotun ta ce majalisar ta take dokar kundin tsarin mulki na 1999 da ke bai wa majalisun jiha damar yin dokoki. A don haka ne ta ce ta soke dokar gaba daya.
Tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar jihar, Nasiru Muhammad Gwarzo ne ya shigar da kara kotun yana kalubalantar dokar majalisar, saboda a cewarsa ba a sanar da shi cewa an koma zaman majalisa ba don yin kudurin, kuma kundin tsarin mulki ya bukaci sai an sanar da shi.
A don haka, kotun ta ce cikin dalilan yanke hukuncin nata har da rashin bin ka'idar sanar da dawowar majalisa.
Maliki Kuliya shi ne lauyan Nasiru Gwarzo, ya ce kotu ta yi abin da ya dace, kuma akwai alamar adalci. "Dama mun jima muna fadar haka."
A yanzu dai gwamnatin jihar Kano na da kwana 90 don daukaka kara.