Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kashe gwamman mutane a Zamfara
Wasu 'yan bindiga sun far wa kauyen Karaye da ke karamar hukumar Gummi a jihar Zamfara da ke Najeriya, tare da hallaka gomman mutane, tare da kona gidaje.
Mazauna kauyen Karaye sun ce ba su taba ganin tashin hankali irin wannan ba.
Sun ce 'yan bindigar sun zo a kan babura dauke da adduna, da bindigogi tare da yi wa kauyen kawanya sun kuma kwashe sa'o'i da dama su na cin karensu ba bu babbaka.
Sun kuma zargi jami'an tsaro ba su kao musu dauki ba, cikin wadanda aka kashe akwai mata da kananan yara da tsofaffi. Wani mazaunin kauyen ya ci karfe shida na yamma barayin suka kewaye garin, ya ce har zuwa hudu na asuba ba su bar garin ba.
Kakakin rundunar 'yansanda a jihar ta Zamfara DSP Muhammad Shehu ya shiadawa BBC cewa ga alama harin na ramuwar gayya ne sakamakon wani artabu da aka yi kwanakin baya tsakanin 'yan bindiga da 'yan sintiri da ake kira 'yan sa kai a yankin.
DSP Shehu ya ce mutane 14 ne suka mutu wasu 10 kuma sun samu rauni, kafin zuwan jami'an tsaro maharan sun tsere.
A halin da ake ciki dai bayanai na cewa dubban mutane sun yi hijira zuwa garin Gummi hedikwatar karamar hukumar sanadiyyar wannan hari.
Masu lura da lamura dai na ganin wannan hari a kauyen Karaye cikin karamar hukumar Gummi, wani babban koma-baya ne ga kwarya-kwaryar zaman lafiya da aka samu a jihar ta Zamfara cikin 'yan watannin nan galibi sakamkon kokarin gwamnatin jihar na tattaunawar sulhu da 'yan bindiga wadanda suka dade suna addabar jihar da ma jihohi makwabtanta.