Sojoji sun kashe jagoran 'yan bindiga a Zamfara

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Runduna ta musamman ta ''Operation Hadarin Daji'' wacce ke karkashin rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kashe wani jagoran 'yan bindiga da ke jihar Zamfara da wasu mabiyansa.

Rundunar sojin kasar ta wallafa hakan a shafinta na Twitter inda take cewa sojojin wadanda aka tura tun a ranar uku ga watan Octoba sun fuskanci hare-hare daga 'yan bindigar amma sojojin sun ce sun yi kokarin dakile hare-haren kuma sun samu nasara a kansu.

Sojojin sun bayyana cewa yayin wannan arangama, dakarun soji hudu sun rasa rayukansu.

A cikin sanarwar, rundunar ta bayyana cewa sojojin sun fara wani sabon atisaye mai suna ''OP Mushare'' a ranar 6 ga watan Octoba domin kama sauran 'yan bindigar.

Sojojin sun ce sun tarwatsa sansanonin 'yan bindigar da ke a Gubarawa da Bawa Daji.

Wasu daga cikin abubuwan da suka kwato sun hada da harsasai na bindigogi, da shanu 177 da wayoyi bakawai da tabar wiwi da sauran abubuwa.

Ko a wannan makon sai da rundunar ta bayyana cewa ta kama wasu manyan mayakan Boko Haram guda 10 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Ta kuma bayyana Modu China a matsayin mai lamba 89 a cikin jerin sunayen mayakan Boko Haram da take nema ruwa a jallo.

Rashin tsaro a Najeriya na daga cikin abubuwan da ke ci wa kasar tuwo a kwarya.

Rashin tsaron ya fi addabar arewa maso gabashin kasar da kuma arewa maso yamma.

A yankin arewa maso gabashin kasar, 'yan kungiyar Boko Haram ne suka fi tayar da zaune tsaye inda kuma a yankin arewa maso yammacin kasar 'yan bindiga da barayin shanu da masu garkuwa da mutane ne ke cin karensu ba babbaka a wasu sassan yankin.