Kudin da masu fada a ji a shafukan sada zumunta ke samu na karuwa

Zoe Sugg, Rita Ora and Rosie-Huntington-Whiteley

Asalin hoton, BBC/Reuters

Bayanan hoto, Zoe Sugg (Zoella) da mawakiya Rita Ora da mai tallar kayan kawa Rosie Huntington- Whiteley duk masu fada-a-ji ne a shafukan sada zumunta
    • Marubuci, Daga Jane Wakefield
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC kan fasaha
  • An wallafa

Kudin da masu fada-a-ji a shafukan sada zumunta ke samu ya yi matukar karuwa a 'yan shekarun da suka wuce, a cewar wani sabon rahoto.

Wani kamfani mai suna Izea ya gano cewa farashin hoto da aka biya don a wallafa shi a Instagram ya yi tashin gwauron zabi daga dala 134 (wato Fam 104) a shekarar 2014 zuwa dala 1,642 (wato Fam 1,276) a shekarar 2019.

Kamfanoni da sana'o'i na biyan kudi masu yawa don masu fada-a-ji a shafukan su yi masu tallar bayanai da labarai da bidiyo, in ji jaridar Business Insider.

Amma wani kwararre ya dage cewar wannan ba ya nufin karshen yadda aka saba yin talla a baya ya zo karshe.

"Talla a shafukan sada zumunta daidai yake da talla ta fatar baki amma dole a rika hada sabon salon talla da yadda aka saba a baya," in ji Yuval Ben-Itzhak, shugaban shafukan sada zumunta na Socialbakers.

Instagram influencers. Average charge per photo post. Charge per sponsored photo post rose from $134.04 in 2014 to $1,642.77 in 2019 .

Rahoton ya duba bayanai da hotuna da bidiyo da aka biya kudi don a wallafa su a kan Facebook da Youtube da Instagram da shafukan intanet, kuma ya duba yadda ake ciniki kan farashin da ake biya tsakanin 2014 da 2019.

Daga kananan masu fada-a-ji- mutane masu mabiya kasa da 100,000 zuwa sanannu, ya gano cewa ana samun kudi masu yawa.

Cikin abubuwan da aka gano su ne:

  • Farashin wallafa hoto a Instagram ya tashi da kashi 44 cikin 100 daga shekarar 2018 zuwa ta 2019 kadai
  • Wallafa bayanai a shafukan sada zumunta ya karu daga dala 7.39 a shekarar 2006 zuwa dala 1,442 a shekarar 2019
  • Wallafa bidiyo a Youtube na da tsada - kuma ya tashi daga dala 420 a shekarar 2014 zuwa dala 6,700 a 2019
  • Farashin wallafa bayani a Facebook ya tashi daga dala takwas a 2014 zuwa dala 395 a 2019
  • A Twitter, wallafa bayani ya tashi daga dala 29 a 2014 zuwa dala 422 a 2019
  • Wallafa bayanai a shafin intanet ya tashi daga dala 407 zuwa dala 1,442

Yayin da mutane ke ta tururwar zama masu fada-a-ji a shafukan sada zumunta, masana'antar na kara fuskantar suka daga masu sa ido.

A cikin watan jiya, wasu masu fada-a-ji uku sun wallafa wasu bayanai a Instagram sun yi tallar wasu magungunan rage kiba da Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta haramta, saboda a cewarta ba su da inganci.

Kuma a farkon shekara, wata hukumar ta yi gargadin cewa wasu masu fada-a-ji na karya wasu dokokin idan ba su bayyana karara cewa hotuna ko bayanan da suka sa a shafukansu, talla ce ba.

Zoe Sugg (Zoella) da mawakiya Rita Ora da Rosie Huntingon- Whiteley na cikin masu fada-a-ji 16 da suka amince su sauya yadda suke saka bayanai a shafukansu.

Kamfanoni da sana'o'i za su ci gaba da zuba kudi a tallace-tallacen shafukan sada zumunta, a cewar bayanai daga Socialbakers.

Influencer articles. Average charge per blog post. Influencers charged $7.39 per blog post in 2006 and $1442.27 in 20 .

Bincikenta ya nuna cewa bayanan da masu fada-a-ji ke wallafawa a matsayin talla sun karu da kashi 15 cikin 100 a bara, ta hanyar amfani da alamar maudu'i #.

Ya yi hasashen cewa kudin da kamfanoni ke biya don talla a shafukan sada zumunta zai karu a 2020, inda hakan ya sa girman masana'antar ya kai dala biliyan 10.

A halin yanzu, Instagram na gwada boye "likes" a kan hotuna da bidiyo a shafin, amma Mista Ben-Itzhak na ganin wannan ba zai yi wani tasiri kan masu fada-a-ji ba.

"Masu fada-a-ji za su iya ganin mutanen da ke bibiyarsu kuma suna yawan bai wa kamfanoni damar ganin wannan bayanin," a cewarsa.

"Babban abin tambaya a nan shi ne idan masu amfani da shafukan za su ci gaba da bibiyar shafukan idan ba sa ganin "likes"."