Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotuna: Labarin addinin Yarsan da ba a san shi ba sosai
Addinin Yarsan na daga cikin tsofaffin addinai a Gabas Ta Tsakiya
Ana kiran addinin Ahl-e Haqq da harshen Larabci, ma'ana mutane masu gaskiya.
An yi kiyasin akalla akwai mabiya addinin miliyan uku a kasar Iran, wadanda yawanci ke zaune a yammacin kasar inda Kurdawa ke da rinjaye. Yayin da wasu mabiya 120,000 zuwa 150,000 ke kasar Iraqi, inda aka fi kiran su da suna Kaka'i.
Wata mai bincike mai suna Behnaz Hosseini, daga jami'ar Oxford wadda ke nazari kan tsirarun addinai a kasashen Iran da Iraqi, a kwanakin baya, ta shafe lokaci mai tsaho cikin mabiya addinin Yarsani a lokacin azumin kwana uku da suke yi.
Wadannan hotunan mallakar Behnaz Hosseini ne