Ko kun san kyautatawa ka iya sa ku yi tsawon rai?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Lauren Turner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Washington
- An wallafa
Shin me kirki zai muku? Ta yiwu ya sanya ku jin dadi da nishadi da inganta lafiyarku? Mai yiwuwa hakan ne, don masu binciken kimiyya sun yi sabon nazari, har ma da tunanin wani abu na daban ciki har da sanya tsawon rai.
Ma'aikatan Cibiyar Kirki da ke Jami'ar California, a birnin Los Angeles sun shirya tsaf don wannan aikin.
Daraktan cibiyar Daniel Fessler ya ce suna duba lamarin ta fuskar kimiyya, suna zama su yi da'ira tare da rike hannayen juna; suna bayani a kan abin da ya shafi kwakwalwa, da yadda ya kamata mutane su rika mu'amala mai kyau—ta hakan ne suke samun kyakkyawan sakamako.
A dan tsakanin nan batun kirki ya ja hankalin mutane da dama. Kuma wani bangare ne na kalaman tsohon Shugaban Amurka Barack Obama, da tsohon dan jam'iyyar Democrat Elijah Cumming wanda ya rasu a watan da ya wuce.
Ya kan ce "Kasancewa jajirtacce na nufin kasasncewa mutum mai kirki, zama mutum mai kirki ba gazawa ko tsoro ba ne. Ba kuma gazawa ba ce don kana taimakon wasu, abin da nake nufi shi ne ka zamo mai kirki ga kowa, don hakan ne mafi dacewa, yana da matukar muhimmanci ka kyautata wa wadanda kake tare da su da ba su girma."
Haka ma Ellen DeGeneres ta taba bayyana alakarta mai ban mamaki da tsohon Shugaban Amurka George W Bush: "Idan na ce ku kyautata wa juna, ba ina nufin mutanen da kuke tare da su kadai ba, ina nufin kowa da kowa ba tare da la'akari da bambancin fahimta da sauransu ba."
Don haka a Ranar Kirki ta Duniya, wato 13 ga watan Nuwamban ko wacce shekara, muna son waiwaye ga abubuwan da suka shafi kirki, da kuma muhimmancinsu.
Wannan shi ne abin da kwararru ke bincike a kai, sun kuma dauke shi da muhimmanci kuma mai yiwuwa abu ne da ya shafi rai da ajali kamar yadda suka fada.

Asalin hoton, Getty Images
Aikin Mista Fessler na duba ne kan yadda za a zaburar da mutane su zamo masu kirki, ta hanyar nuna musu wani dan abu da aka yi da ya shafi kirki da wadanda lamarin ya shafa.
"Ina ganin kamar tsarin da muke tafiyar da rayuwarmu a halin yanzu bai dace ba, ina nufin a nan gida Amurka da sauran sassan duniya; abin da muke gani na kara rura wutar rashin zaman lafiya tsakanin al'umma kama daga masu bambancin siyasa da addini."
Ya kara da cewa ''Kirki wani yanayi ne da ka ke ji a cikin ranka, ba tare da an koya maka ba ka ke kuma yin shi ga mutane ba tare da ka sani ba kuma hakan na sanya wasu su karu.
"Haka a dayan bangaren rashin kirki yanayi ne da mutum ke imani da shi, da ke sanya rashin mu'amala mai kyau da mutane. Yanayi ne da yawancin mutanen da ke mu'amala da shafukan sada zumunta kan samu kansu a ciki idan sun yi karo da wani abu da bai musu dadi ba".
Fessler ya ce dabi'ar kirki ba sabon al'amari ba ne, kuma akan samu mutane masu dacin rai da saurin fusata wadanda ba lallai su mutunta sauran mutane ba. Cibiyar dai an samar da ita ne da tallafin Fam miliyan 16 da gidauniyar Bedari, wadda malaman falsafa Jennifer da Matthew Harris suka samar, ta bayar.
Mista Harris ya ce ana bukatar yin nazari don fahimtar muhimmancin kirki a duniya, tare da nakaltar yadda za a kitsawa jama'a dabi'ar yin hakan.
Wasu daga cikin ayyukan da cibiyar za ta yi sun hada da;
- Duba yadda za a samar da kirki ga jama'a
- Da nazari kan wadanda ba su cika damuwa da yin dabi'ar kirki ba, da sauya musu wannan akida
- Da yin bincike mai zurfi kan yadda kirki zai inganta rayuwar mutane da rage musu damuwa

Asalin hoton, UCLA
Har wayau, ana kokarin bai wa dalibai horo na musamman da mutanen birnin Los Angeles.
Sai dai Mista Fessler ya amince yanayi kan sanya mutumin kirki ya zamo kishiyar hakan, yanayin da babu dama ka kalubalanci abu kuma babu yadda za ka yi.
"Zama tare da mutanen da suke mutuntaka da halin ko in kula, ba tare da girmamawa ba wannan zai iya takaita tsawon rayuwarka ba shi da kyau sam a gare ka," inji Fessler.
"Haka kuma girmamawa da mutuntawa da kirki da wasu suka yi maka wadannan sinadarai ne na tsawon rai a gare ka."
'Sakon gaggawa'
Wata malama a Jami'ar Columbia Dr Kelli Harding ta dade tana bincike a kan kirki da ta ke rubutu akai mai suna, The Rabbit Effect.
Ta bayyana cewa: "Kirki yana taimakawa wajen gudanar jini, da rage hawan jini, ya inganta rayuwar mutane su yi tsawon rai da rayuwa mai inganci. Abin ban sha'awar shi ne kirki baya yawa ko kadan, babbar illar shi ne a ce babu baki daya kuma a kyauta ake samnunsa ba tare da an biya wani abu ba."
Da take karin haske a kan sabon littafin nata, Dr Kelli ta ce ta taba jin an yi bincike kan halayyar Zomo a shekarun 1970. "Wani bangare an samu kyakkyawan sakamako, wani kuma akasin hakan, shi ya sa na ke son sanin dalilin hakan. Bincikena ya gano min zomon ya kasance cikin kwanciyar hankali sakamakon kulawar da wani mai bincike ya ba shi.
"Na kadu matuka a matsayina na likita, jikina ya ba ni akwai wani sakon gaggawa da ba a isar ba, wannan abun kuwa ba komai ba ne sai kirki, taimako da zai inganta rayuwarsu."

Asalin hoton, Getty Images
Dabarun samun ingantacciyar rayuwa
Daga Gabriella Van Rij, kwararre a wannan fanni
- Ka dinga sauraren abin da mutane ke fada, ta haka za ka samu saukin fahimtar abin da ake nufi maimakon ka yanke hukunci kai tsaye
- A duk lokacin da aka yi maka magana cikin fushi, ka yi kokarin tausasa harshenka idan za ka ba da amsa, ka sassauta muryarka cikin nishadi ka tambaye shi abin da ke damunsa
- A koda yaushe ka yi kokarin janyo mutanen da lamari ya shafa, idan kana yin haka zai nuna kana ba su daraja. Mutane ba sa jin dadi idan ba a nuna musu kauna ko kulawa ba
- Daukar mataki. Ka tabbatar ka fahimci yanayin da ake ciki idan wani bau ya faru na rashin kyautatawa ba lallai sai ya shafe ka kai tsaye ba, idan an fusata ka yi kokarin nutsuwa don kar ka dauki matakin da bai dace ba












