Musulmi na bikin Maulidi a fadin duniya

Asalin hoton, A taron Maulidin Nyass mutumin ya yi kalaman
A ranar 12 ga watan Rabiul Awwal, wani bangare na al'ummar Musulmi na gudanar da bukukuwan Maulidi domin murnar zagayowar ranar da aka haifi Manzon Allah, Annabi Muhammad SAW.
Sai dai ba dukkan Musulmi ne ke bikin ranar ba, saboda sabanin fahimta.
Sheikh Umar Sani Fagge ya shaida wa BBC fa'idar ranar, inda ya ce wannan rana ce mai matukar muhimmanci.
Ya ce rana ce ta gode wa Allah kan baiwar da ya yi wa al'ummar Musulmi ta Annabi Muhammadu.
"Musulmi sukan tuna wannan rana da aka haifi Manzon Allah domin yin godiya ga Allah kan ni'imar samun Annabi SAW," inji shi.
Shehin malamin ya ce wannan rana na da matukar muhimmanci saboda shi kanshi Annabi SAW ya kan azuminci ranar da aka haife shi.
"An tambaye shi saboda me yake azumi Litinin, ya ce 'saboda wannan ranar aka haife ni'".
Ya ce wannan ranar ta kunshi nuna so da kauna da tunatar da Musulmi game da kyawawan halayen Annabi SAW da yadda ya rayu domin a yi koyi da shi.
Shehin malamin ya ce abubuwan da ya dace a yi a wannan lokaci sun hada da karatun Al-Kur'ani da karanta Sira ta Annabi SAW da yin zikiri da salati ga Annabi SAW, da yabonsa.
Akwai dai wani bangare na Musulmi da ke sukar maulidi, inda suke cewa Annabi da Sahabbansa ba su yi ba.












