An kama 'dangin' Baghdadi a Syria

Asalin hoton, Getty Images
Turkiya ta ce ta kama wasu dangin Abu Bakr Al Baghdadi jagoran ISIS da aka kashe makon da ya gabata.
Hukumomin Turkiya sun kama yayarsa Rasmiya Awad da mijinta a yankin arewacin Syria da ke karkashin ikonta inda suke zaune tare da sauran danginta.
Turkiya ta ce ta kama ta ne domin tatsar bayanai daga bakinta, yayin da kuma kasashen yammaci suka nuna shakku kan ikirarin Turkiya.
Ko da yake kasashen na yammaci sun amince za a iya tasar bayanai game da rayuwar yayanta Baghdadi da kuma tsarin kungiyar ISIS.
Jagoran IS dai ya kashe kansa ne bayan samamen da dakarun Amurka na musamman suka kai a arewacin Syria, kuma a wani sakon murya da kungiyar IS ta fitar a intanet ta tabbatar da mutuwar jagoran nata tare da alwashin daukar fansa kan Amurka.
Baghdadi ya kafa daular musulunci a Syria tsakanin 2014 zuwa 2017 kafin dakarun Amurka da Syria da Iraqi da na Kurdawa su tarwatsa IS.

Asalin hoton, Getty Images






