Jami'ar Kaduna ta dakatar da malami kan 'lalata da dalibai'

An wallafa

Mahukuntan Jami'ar jihar Kaduna sun sanar da matakin dakatar da daya daga cikin malamansu, bisa zargin neman yin lalata da dalibai.

Rahotanni sun ce a ranar Talata ne wata daliba ta gudanar da zanga-zangar mutum daya, inda ta zargi jami'ar da zama mafaka ga wanda ake zargi da aikata lalata da dalibai.

Mataimakin shugaban sashen kula da harkokin dalibai a Jami'ar, Dr Tukur Abdulkadir ya ce tuni bincike ya yi nisa kan zargin.

Ku latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron sautin muryar.