Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya tana tuhumar 'yan Birtaniya biyu kan laifuka 16
Hukumar da ke yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya EFCC ta tuhumi wasu 'yan kasar Birtaniya biyu da laifuka 16 na fitar da kudi ba bisa ka'ida ba.
Hukumomi sun ce wadanda ake zargin wato James Richard Nolan da kuma Adam Quinn daraktoci ne a kamfanin P&ID.
Ba a jima ba da kamfanin ya yi nasara kan karar da ya shigar yana neman diyya daga gwamnatin Najeriya, kuma kotu a Birtaniya ta umurci gwamnatin da ta bashi diyyar dala biliyan tara.
Lauyan da ke kare Mista Nolan da Mista Quinn ya musanta zargin da ake yi wa wadanda ya ke karewa.
A yanzu ana kan neman Mista Quinn ruwa a jallo, to sai dai tuni a ka sakaya Mista Nolan a kurkuku kafin ya cika sharudan beli.
A sanarwar da hukumar ta EFCC ta fitar ta ce kamfanin P & ID ya yi rufa-rufa kan dala 125,000 da ke wani asusun ajiyarsa da ke kasar.
Bugu da kari hukumar ta ce kamfanin bai fayyace wa ma'aikatar da ke kula da harkokin kasuwanci duka ababen da ya keyi a kasar ba.
Wannan dai wani sabon shafi ne na rikici tsakanin gwamnatin Najeriyar da P & ID, wanda aka soma tun a shekarar 2010 kan wata yarjejeniyar samar da iskar gas.
A cewar kamfanin, rashin cika sharuddan yarjejeniyar a bangaren gwamnatin Najeriya ya sa ya tafka mummunar asara.
To amma a na ta bangaren, gwamnatin ta ce dama akwai lauje cikin nadi, ta kuma zargi cewa dama kamfanin ya kulla yarjejeniyar ne da fatan hakan ta faru.