Bam ya kashe mutum 62 a masallacin Juma'a a Afghanistan

Asalin hoton, EPA
Akalla mutum 62 da biyu ne suka mutu sannan gommai suka jikkata a wani harin bam ana tsaka da sallar Juma'a, a Afghanistan, in ji mai magana da yawun yankin Nangarha .
Karfin tashin bam din ya yi awon gaba da rufin gidaje, kamar yadda wani wanda ya shaida yadda al'amarin ya faru, ya fada wa BBC. Babu wani wanda ya dauki alhakin harin.
Wannan harin dai na zuwa ne bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan fararen hular da suka mutu a Afghanistan ya zarce hankali.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe fararen hula 1,174 tsakanin Yuli da Satumba, wani lokacin da aka fi kashe mutane a cikinsa a tsawon shekaru 10.
Attaullah Khogyani, mai magana da gwamnan lardin ya shaida wa BBC cewa mutum 62 ne aka kashe sannan mutum 36 sun samu raunuka a harin da aka kai wa masallata.
Masallacin da aka kai harin ya kasance a gundumar Haska Mina, kilomita 50 daga birnin Jalalabad.

Asalin hoton, Reuters








